Iran ta farmaki mafi girman tashar makamashin gas ta duniya a Ƙatar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba ƙasar Iran ta kai hari kan mafi girman tashar fitar da iskar gas mai ruwa (LNG) a duniya dake Ƙatar, a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai mata a tashar gas ɗinta ta South Pars.

Harin ya shafi Ras Laffan Industrial City, inda aka samu wuta da lalacewa mai yawa, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Ƙatar ta bayyana.

Da take abbatar da faruwar al’amarin ma’aikatar ta ce jami’an kashe gobara suna kan aikin kashe wutar ta biyo bayan harin.

Wannan harin na zuwa ne bayan wasu hare-hare a filayen makamashi a yankin, yana kara tsananta rikicin da ke da alaƙa da makamashi.

Haka kuma, farashin mai da gas sun tashi saboda tsoron katsewar samar da makamashi a duniya.

Harin na daga cikin rikicin Gabas ta Tsakiya da ke tsakanin Iran da Isra’ila, inda kowanne ɓangare ke kai hari a tashoshin makamashin juna.

By Babaji