
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fraministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa ce kaɗai taek da alhakin kai Faransa a tashar na ƙasar Iran yayin ake cigaba da shiga halin fargaba kan kai wa tashoshin makamashi hari a Gabas ta Tsakiya.
Waɗannan hare-hare sun yi sanadiyyar tashin farashin dangogin makamashi, sannan Shugaba Donald Trump ya ce bai sanda su ba gabanin ƙaddamarwa.
A wani labarin, Netanyahu ya ce ƙasarsa, ba za ta sake kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Iran ba. Yana magana ne bayan wani gargadi da shugaba Trumo ya yi masa kan sake yin hakan.
Wani harin da Isra’ila ta kai kan cibiyar iskar gas ta South Pars ta Iran a ranar Laraba, da kuma martanin da Iran din ta mayar, sun haifar da tashin gwauron zabin farashin gas da man fetur a kasashen Turai.
Da yake magana a wani taron manema labarai, Netanyahu ya yi watsi da zarge-zargen cewa shi ya yi wa shugaba Trump angiza mai kantu ruwa, wajen kai wa Iran din hari.
Ya bayyana cewa, “yanzu har akwai wanda ke tunanin cewa wai wani ne zai faɗa wa Shugaba Trump ga abun da ya kamata ya yi?… Ya ce, shugaba Trump na ɗaukar mataki ne akan abin da ya ke ganin shi ne daidai ga Amurkawa da kuma gobenmu baki daya.”
