Jabun magunguna sun fi Boko Haram kisan ’yan Nijeriya – NAFDAC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta yi wani gagarumin gargaɗin cewa jabun magunguna, da abinci mara kyau, da kayayyakin gyaran fuska da ba a tantance ba, sun fi kashe rayuka a Nijeriya fiye da rikicin Boko Haram.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Dr. Martins Iluyomade, Daraktan Bincike da Tabbatar da Doka na NAFDAC, yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata bayan wani gagarumin aikin tabbatar da ingantacin kayayyaki a kasuwar Legas.

Tsawon kwanaki biyar ya kai ga kama sama da katon 10,000 na lalataccen tumatur ɗin gwangwani da kayan kwalliya marasa rajista, waɗanda yawancinsu a cewar hukumar ta NAFDAC, na haifar da babbar illa ga lafiyar masu amfani da su.

“Zan iya cewa a hukumance magunguna marasa inganci, kayan kwalliya, da abinci mara kyau sun zarce adadin mutanen da Boko Haram ta kashe,” inji Dr. Iluyomade.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa hukumar ta tsaya tsayin daka don tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya suna amfani da kayayyakin masu inganci tare da tabbatar da amincin su.”

Yayin da ta’addancin Boko Haram ya mamaye kanun labaran duniya sama da shekaru goma, gargaɗin NAFDAC irin illar da gurɓatattun kaya ke yi wa al’umma.

Nijeriya ce ta 6 a ƙididdigar ta’addanci ta duniya a shekarar 2025, wanda ya kai kashi 6 na mace-macen ta’addanci a duniya a shekarar 2023, a cewar bayanan hukuma.

Alƙaluman da Asusun Tallafawa Jama’a na Duniya (GCERF) ya yi ya nuna cewa tun daga shekarar 2007, sama da mutane 11,000 ne aka kashe ta hanyar tayar da ƙayar baya a Nijeriya, tare da asarar miliyoyin daloli.

Duk da haka, Dr. Iluyomade ya dage cewa adadin waɗanda suka mutu daga magungunan jabu, gurɓatattun abinci, da kayan gyaran jiki ya fi yawa, saboda galibin waɗannan mutuwar suna faruwa ne cikin nutsuwa, ba tare da kan hankalin kafafen yaɗa labarai kamar yadda ta’addanci ya yi ba.

Rahoton na GCERF ya yi nuni da cewa shekaru da dama da Nijeriya ta yi fama da tashe-tashen hankula—musamman a Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Yamma—ya lalata tattalin arzikin cikin gida da kuma taɓarɓarewar tsarin mulki.

Hukumar ta GCERF ta kashe dala miliyan 11.75 tun daga shekarar 2016 don magance musabbabin tashin hankalin, amma NAFDAC ta yi gargaɗin cewa yaƙi da jabun kayayyakin yana buƙatar kulawar ƙasa da kuma saka hannun jari cikin gaggawa.

By ukarofi