Wani harin jirgin sama na sojojin Isra’ila ya harbe wani sansanin ‘yan jarida kusa da Asibitin al-Shifa a birnin Gaza, inda aka kashe ‘yan jarida shida, ciki har da mashahurin ɗan jaridar Al Jazeera, Anas al-Sharif.
Bayanai daga asibitin al-Shifa sun tabbatar da mutuwar wasu ƙungiyoyin ‘yan jarida, waɗanda suka haɗa da Anas al-Sharif, da Mohammed ƙreiƙeh, Ibrahim Zaher, Mohammed Noufal, dukkaninsu ma’aikatan Al Jazeera da kuma wasu ma’aikata masu zaman kansu biyu, Moamen Aliwa da Mohammad al-Khaldi.
Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa, Anas al-Sharif shi ne shugaban wata ƙungiyar mayaƙan Hamas da ke kai hare-hare kan Isra’ila, amma Al Jazeera ta musanta wannan iƙirari tana mai cewa, an kashe shi ne a matsayin ɗan jarida mai aiki.
ƙungiyoyin kare ‘yancin ‘yan jarida da Majalisar ɗinkin Duniya sun yi Allah wadai da harin, suna kiran a gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar lamarin.
A Gaza, dubban mutane sun hallara don gudanar da jana’izarsu tare da yin zanga-zanga, inda suka rera ƙara da suka yi wa firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu. Bugu da ƙari, an gudanar da zanga-zanga a biranen duniya da dama ciki har da Ramallah, Berlin, Dublin da Washington DC, don nuna rashin amincewa da harin.
