
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Kalifan Ɗarikar Tijjaniyya kuma Jagoran Majalisar Ƙolinta, Sheikh Sidi Ali Belarabi Tidjani, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Abuja a matsayin wani bangarena ziyararsa ta zuwa Nijeriya a hukumance.
Sheikh Tidjani ya isa Nijeriya ne a ranar Alhamis tare da wata tawaga daga Zawiyar Kalifanci da ke Aïn Madhi a Aljeriya, bayan wata gayyata ta musamman daga jagororin Tijjaniyya a Nijeriya.
A yayin haka ne ya yi tsokaci kan daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Aljeriya, tare da nuna kwaɗayin ƙarfafa alaƙar ta hanyoyi da dama da suka shafi ci-gaba.
Tawagar ta haɗa da fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya a Nijeriya, Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi, Babban Khalifan Tijjaniyya na Aljeriya, Sheikh Ali Al-Arabi, da kuma babban malamin addini daga Senegal, Sheikh Muhammad Al-Mahy.
Ziyarar ta gudana ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda shugabannin suka gana da Shugaba Tinubu kan batutuwan da suka shafi addini, haɗin kai da kuma zaman lafiya.
Hotunan da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar sun nuna yadda aka yi tarbar shugabannin cikin girmamawa, lamarin da ya janyo hankalin jama’a tare da ƙara nuna kyakkyawar alaƙa tsakanin Nijeriya da manyan jagororin ɗarikar Tijjaniyya a Nahiyar Afirka.
Kalifan ya kuma yi addu’ar fatan samun ƙarin albarka acikin ‘yan kasashen biyu wajen samun zaman lafiya, haɗin kai, soyayya da ɗorewar al’amura.
