Jakadan Sin dake Nijeriya, ya halarci bikin buɗe ajin horas da jami’an APC ta yanar gizo

Daga CMG HAUSA

Ran 1 ga watan nan na Satumba, hukumar tuntubar ƙasashen waje ta kwamitin tsakiyar JKS, da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, da jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, sun shirya gabatar da ajin horas da mambobin jam’iyyar APC ta yanar gizo da kuma ta zahiri, bisa taken “Ƙara ƙarfin jami’iyya mai mulkin ƙasar don ba da jagoranci”.

Mataimaki ga ministan hukumar Li Mingxiang, ya halarci bikin buɗe zaman ta kafar bidiyo tare da ba da jawabi.

Kaza lika shi ma jakadan Sin dake ƙasar Cui Jianchun ya ba da jawabinsa.

Sai kuma manyan jami’ai fiye da 30 na jam’iyyar APC, ciki har da mataimakin darektan jam’iyyar Festus Fuanter, duk sun halarci bikin.

A jawabinsa, Li Mingxiang ya nuna cewa, Sin na fatan hadin kai da Najeriya, da mutunta muradunsu masu tushe, da abubuwan da suke jawo hankalinsu, don tabbatar da shawarwarin raya duniya baki ɗaya, da shawarwarin ba da tabbaci ga tsaron duniya, da gaggauta kafa kyakkyawar makomar al’ummar Sin da Afrika ta bai ɗaya a sabon zamani.

A nasa ɓangare, mataimakin darektan jam’iyyar APC Festus Fuanter ya nuna cewa, JKS wata jam’iyya ce mai ƙarfin jagoranci dake da tarihi shekaru 101, kuma tana da tasiri matuƙa a duniya, APC jami’iyya ce da ba ta jima da kafuwa ba.

Ya ce al’ummar Sinawa sun samu nasarar yaƙi da talauci, da tinkarar COVID-19, da farfaɗo da tattalin arzikinta, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Xi Jinping, abin da ya kamata Najeriya ta yi koyi da shi.

Ya ce Najeriya za ta ci gaba da kara mu’ammala da ɓangaren Sin, don koyon fasahohin JKS wajen gudanar da harkokin ƙasa.

Fassarawar Amina Xu