Sin ta yi bikin cika shekaru 77 da cimma nasarar yaƙin ƙin harin Japanawa

Daga CMG HAUSA

A yau Asabar ne ƙasar Sin ke gudanar da bikin cika shekaru 77, da cimma nasarar yaƙin kin harin Japanawa, da yakin nuna adawa da ‘yan mulkin danniya na duniya.

A gundumar Shijingshan dake nan birnin Beijing, jami’an hukuma, da dakarun rundunar ‘yantar da al’umma, da wakilan dalibai, sun yi tattaki zuwa wurin da mahara Japanawa suka kafa tudun harba makamai.

Kaza lika, sun ziyarci daya daga dakarun da suka halarci yakin kin jinin harin Japanawa mai shekaru 97 a duniya, wanda ya ba su wasu labarai game da ɗauki ba dadin da aka yi, domin daƙile harin Japanawa.

A birnin Shanghai kuwa, gwamman Sinawa sun taru, a ɗakin tunawa na Songhu Kangzhan, wanda aka gina domin tunawa da lokacin ɓarkewar babban yaki a karon farko, domin daƙile farmakin dakarun Japan.

Jama’ar da suka taru, sun kuma yi shiru na dan lokaci, domin girmama sadaukarwar da ‘yan mazan jiya suka yi domin kare ƙasar Sin.

Kaza lika a yankin musamman na Hong Kong ma, an gudanar da makamancin wannan biki, wanda ya kunshi buga taken ƙasa, da daga tutar ƙasa, da jinjina ga waɗanda suka rasa rayukan su, yayin yakin na daƙile harin Japanawa, a babban lambun ƙasa dake birnin, taron da ya samu halartar babban kantoman yankin John Lee, da sauran jami’an sassa, da ‘yan majalissu.

A ranar 2 ga watan Satumbar shekarar 1945 ne ƙasar Japan, ta sanya hannu kan takardar miƙa wuya a yakin duniya na II, kusan makwanni 2 bayan ta ayyana amincewa da hakan.

A shekarar 2014 kuma, ƙasar Sin ta sanar da ranar 3 ga watan Satumbar ko wace shekara, a matsayin ranar tunawa da cimma nasara kan dakarun ƙasar Japan.

Mai fassara: Saminu Alhassan