Ya Kamata ASUU da gwamnati su saka lamarin ɗaliban Nijeriya a gaba

Sama da watanni shida kenan da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta tsunduma yajin aikin makonni huɗu da farko inda daga baya suka fara na gama-gari domin neman a biya musu buƙatunsu.

A fili ƙarara dole a nuna rashin jin daɗi da rashin jajircewa da gwamnatin tarayya da ƙungiyar suka yi wajen cimma yarjejeniya da kawo ƙarshen yajin aikin. Gwamnati da ASUU sun kuma nuna rashin tausayawa halin da iyaye da ɗalibai ke ciki da kuma neman ilimi mai inganci ga matasanmu.

A ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne ƙungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargaɗi ga gwamanatin Nijeriya na tsawon wata guda.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka ƙulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na ƙasar.

Wasu bayanai sun nuna cewa ƙungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Nijeriya mulkin dimokuraɗiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

Yajin aikin ya fi yin tasiri a kan ɗalibai waɗanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata ƙungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin ƙasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

A halin yanzu, da zarar an ambaci sunan ASUU, yajin aiki ne kawai ake gani. ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar ƙarshe da ta ke bi domin tilasta wa gwamnatin Nijeriya biya ma ta buƙatunta.

Amma duk da haka, maimakon a yi aiki da gaske wajen cimma yarjejeniya a tsakaninsu, gwamnatin tarayya da ASUU sun yi ta yaƙar junansu, suna nuna ƙarya da bayanan ƙarya ga al’ummar Nijeriya.

Misali, a ranar 17 ga Agusta, 2022, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanar da ‘yan Nijeriya cewa, an warware duk wata matsala tsakanin gwamnati da ASUU, in ban da albashin watannin da ASUU ta shiga yajin aikin, wanda ya ce, shima gwamnati za ta warware don abin ya hana yajin aikin. Ministan ya ci gaba da neman ɗaliban da su kai ƙarar ƙungiyar ASUU domin dakatar da yajin aikin.

A halin da ake ciki, ASUU ta musanta cewa an tava tattaunawa da ministan a kan basussukan albashi, inda ta ƙara da cewa, ba a cimma matsaya ba kan muhimman batutuwan da suka sanya yajin aikin.

Dukka ɓangare biyu dole ne su sassauta matsayinsu. Ko ta yaya, gwamnatin tarayya ba ta nuna cikakken imani da jajircewa wajen aiwatar da rahotannin kwamitocin tattaunawa guda biyu – Farfesa Jibril Munzali kwamitin Mayu, 2021 da kwamitin Farfesa Nimi Brigg da ya kammala ba, wanda ta ƙaddamar a farkon taron warware yajin aikin na yanzu.

Kasancewar ’yan Nijeriya sun karaya kan yadda ake tafiyar da yajin aikin kawo yanzu, gwamnatin tarayya da ƙungiyar ASUU dole ne su dakatar da wannan fafatawa na neman kuɗi domin babu wani bayani mai ma’ana kan yajin aikin da ya ɗauki tsawon lokaci ana yi. Lamirinsu a matsayinsu na masu kishin ƙasa dole ne ya ɗauki matakin hankali.

Dole ne ɓangarorin biyu su gane cewa Nijeriya ba za ta iya ci gaba da yin wasa da vangaren ilimi ba, kamar yadda ta ke bayyana makomar ƙasar da kuma al’ummomin da ba a haifa ba. Dole ne kawai a yanke hukunci bisa maslahar ƙasa kuma tare da fahimtar juna.

Blueprint Manhaja ta yi kira ga gwamnati da ta ɗauki kwararan matakai don kawo ƙarshen yajin aikin da ke barazana ga makomar matasanmu. Ya kamata shugaba Buhari ya shiga tsakani kai tsaye ba tare da wani mai shiga tsakani na ministoci a tattaunawar ba.

Su kuma ASUU, dole ne su gane cewa babu wanda ke samun nasara ɗari bisa ɗari a duk wata tattaunawa, kuma su kasance da haƙiƙanin abin da kowace gwamnati za ta iya cimmawa ta fuskar jin daɗin ma’aikatan ilimi da kuɗin tallafin jami’o’in ƙasar nan. Har ila yau, lokaci ya yi da Majalisar Dokoki ta ƙasa, tsaffin shugabannin ƙasa, sarakunan gargajiya, da malaman addini su ma su nemi hanyar shiga tsakani don kawo ƙarshen yajin aikin da ake fama da shi a halin yanzu da kuma samar da mafita mai ɗorewa.

Abin da ke tattare da shi a nan ba zai iya barin ƙungiyar ASUU da gwamnatin tarayya kaɗai ba. Ya kamata duk wani mai hannu da shuni ya saka baki.