Ambaliyar ruwa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Yayin da watan Agusta ya yi bankwana mutane na lissafin asarar da su ka tafka a sanadiyyar ambaliyar ruwa. Ba birni ba ƙauyuka, duk kanwar ja ce a sassa da dama. Duk da ba sabon abu ba ne ambaliyar ruwa amma duk lokacin da ya faru sai ya zama babban labari don ya kan haddasa asarar rayuka da dukiya.

Ambaliyar bana fa ba ta Nijeriya ba ce kadai don a qasar Pakisatan lamarin ya yi tsanani aiunun inda ɗaruruwan mutane su ka rasa ransu. A yanzu haka Pakistan na jiran tsammanin samun ɗauki daga ƙasashe don batun tallafawa jama’a ko ma a ce tsugunar da mutane. Can Daular Larabawa ma sun yi fama da ambaliyar da ta kai ga dole sai da a ka ƙaurar da waɗanda lamarin ya shafa zuwa wasu sassa kafin sake dawo da su.

Hotunan da ke yawo a yanar gizo na nuna yadda ambaliyar ke mayar da manyan layuka na tsakiyar gari su koma tamkar koguna. Haka za ka ga masu motoci da babura na yunƙurin kutsawa don samun wucewa. Haƙiƙa akwai inda hakan ya yi awon gaba da motocin ko kuma ka ga mota ta mutu don ruwa ya ratsa ta don haka inji sai ya buga.

Akwai inda ruwan kan share gonaki ya zama duk amfani ya tafi. Duk iftila’i indai zai tsaya a kan dukiya da sauqi amma gaskiya a duk inda a ka samu gagarumar ambaliyar ruwa to kuwa ba mamaki a samu asarar rayuka. Rayukan kan ba na ‘yan adam ba kaɗai har ma da dabbobin gida da na dawa. Don haka a ke addu’a Allah ya ba da damuna mai albarka.

Cikin hukuncin Allah za ka ga wata shekara kusan da ƙyar suke samun ruwan da zai wadaci gonaki wani lokacin ma sai ya kai ga an fita sallar roƙon ruwa. Shuka ta yi yaushi mutane su shiga firgicin barazanar fari. Wata shekarar kuma ruwan ne zai yi ta sauka kamar da baƙin kwarya har kusan sai an yi ta addu’ar ruwan ya tsaya. Hakan shi ya faru bana a wasu sassa.

Abin da ya dau hankali na, na ɗauki wannan darasi a wannan mako shi ne yadda ambaliyar ta auku a Kano. Wannan lamari ya yi tsanani ainun don gine-gine sun ruguje hakanan tituna sun malale da ruwa. Mutane kan cije su shiga cikin ruwan don tafiya harkokin su na yau da kullum.

Hotunan da na gani na motoci sun tsunduma ruwa ga ‘yan keke-napep na ƙoƙarin ratsa ruwan ya girgizani ainun. Hoton ya zauna a zuciya ta har na tuna wata rana ina haramar dawowa Abuja na ɗauko mota ina tafiya sai na hango mutane a tsaye a can gaba na ƙara matsawa da tunanin ko wata mota ce ta samu matsala ashe ba haka ba ne.

Haƙiƙanin abin da ya faru shi ne ruwan sama ne ya yi kukan kura ya hauro kan babban titin ya ratsa shi zuwa ɗaya gefen ya na rimi ya bi sabuwar hanyar sa tamkar babban kogi ya kawo ruwa. Ba ƙaramar kasada ba ce mutum ya yi yunƙurin keta ruwan da sunan neman wucewa. Irin wannan kasada ka iya haifar da komai don zai yiwu ruwa ya janye motar shikenan sai yadda hali ya yi.

Da na jira don ganin lamarin ko zai lafa amma ba alamun hakan sai na yi sallama da masu jira na juyo gida na kwance damarar tafiyar. Abun mamaki titin da a ke bi na taraiya a ga irin wannan yankowar ruwa daga daji ko cikin gonaki da irin wannan ƙarfi mai kama da ƙaramar igiyar teku.

A bana na fara maida hankali kan lamarin ambaliyar ruwa bayan cin karo da yadda ruwa ya hauro kan tagwayen titin Abuja zuwa Keffi inda kwatsam ina cikin tafiya sai na ji na faɗa cikin ruwa mai yawa da aƙalla za a ce ya shanye tsawon taya.

Da farko na ɗauko ɗan guri ne kaɗan amma da na cigaba da tafiya sai na gane babban lamari ne hakan ya tilasta gwada hannun da ba nawa ba nan ma haka lamarin ya ke har na hango kai tsaye ina tunkarar wata babbar mota da ta ke kan hannunta. Wannan ya sa na koma gefen titin har motar ta wuce daga nan na sake yunƙuri na dawo hannu na.

Ban yi nisa ba na ga kamar ruwan na ƙaruwa ne don haka na yi ƙoƙarin samun bakin wata kasuwa zamani “plaza” na tsaya don nazarin yadda zan yi na wuce wajen nan ba tare da samun matsala a mota ta ba. Wani direba ba niki-niki da lodi ya tsaya a kusa da ni ya kunna taɓa don jiran raguwar ruwan. Nan na share kimanin sa’a biyu ina jira har wasu motoci masu kama da yanayin mota ta, su ka yi ƙundumbala su ka ratsa ruwan don haka ni ma na yi harama na shiga ina ta tafiya har da yardar Allah na isa tudun mun tsira a daidai Unguwar Nyanya ta Abuja.

Washegari da na tambaya ashe haka mutanen yankin ke fama in an tsuga ruwan sama. A ka ba ni labari ai a ranar ko kafin ita ruwa ya yi awon gaba da wani mai tuqa Babur. Hakanan an ba da labarin ambaliyar ta tilastawa wasu barin wasu sassan Unguwar Maraba don ruwa ya shanye gidajen su.

Ba ƙaramin lamari ba ne mutum ya na mallakar gidan kan sa a yankin ya fice ya sau ladansa sai in ya zama dole kamar funkantar irin ƙalubalen ambaliyar.

Hukumar kula da sauyin yanayi ta Nijeriya ta ankarar da jama’a cewa bana za a samu ambaliyar ruwa don haka a ɗauki matakan ƙaurace wa sassan da a kan samu ambaliyar.

Ai shi ruwan ambaliya ba a tare ma sa hanya sai dai a dau matakan zama a inda babu barazanar. Hakanan sai mutane sai qara ɗaukar matakan tabbatar da magudanan ruwa ba su zama a toshe da shara ba. Gaskiya duk inda ka ga an yi ambaliya a gefen titi, to za ka tarar a mafi yawan lokuta an toshe magudanan ruwa ne. Wani abun kuma shi ne duk arahar fili a inda ke da barazanar ambaliya to a kaucewa saya don araha za ta haddasawa mutum tsada.

Jami’an tsabtace muhalli na ƙarfafa aikin gayya don share magudanan ruwa kafin damuna don hakan ya taimaka wajen rage kaifin ruwan da zai juye zuwa ambaliya. Ai ba wani mamaki ga jama’ar da ta cike magudanan ruwan ta da shara ta wayi gari ambaliyar ruwa ta rutsa da ita.

Hukumomin tsara birane ya kamata su matsa kaimi wajen tabbatar da an samu wadatattun magudanan ruwa a duk inda a ka ware za a yi sabbin gidaje. Kazalika duk waɗanda su ka toshe magudanan ko su ka biri a ka cutar da magudanan nan a dau mataki mai tsauri a kansu ta hanyar hukunci daga kotun tafi da gidanka.

Kammalawa;

Yana da muhimmanci jami’an kare lafiyar muhalli su dawo aikin wayar da kan jama’a gadan-gadan muhimmancin kauce wa toshe hanyoyin ruwa don yin gida, noma ko wata sana’ar ta daban. Mutane kuma su yi kishin lafiyarsu, su fito don taimakon kansu da kansu.

Ba zai taba yiwuwa gwamnati ta iya biya wa jama’a dukkan buqatunsu na tsabatace muhalli ba. Idan mutum ya zo sayan fili to ya gayyato kwararrusu zo su duba filin da ba da shawarar ko filin ya aminta daga faɗawa sassan ambaliyar ruwa.

Hakanan a guji sare bishiyoyi da ke ƙara ƙarfin ƙasa da gonaki don hakan ya zama darasi ga kananan manoma ko ma masu amfana da daji su kiyaye don kar a wayi gari manomi ya samu gonarsa ta koma fadamar ruwa ko fadamar yashi.

Mutane su riƙa bin kafafen labaru don sanin sabbin dabarun kauda bara ga faɗawa tarkon ambaliya.