Duk matashi mai son zama Biloniya da Naira 1,500 kacal, ya zo na koya masa – Inji matashin attajiri Jamilu Abubakar

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Zaman kashe wando a tsakanin matasan wannan zamani kusan ba sabon lamari ba ne, la’akari da yadda dubban matasan da suka kammala jami’oi da manyan makarantun gaba da sakanidiri ke kammalawa ba tare da ayukkan yi ba, domin dogaro da kai. Kodayake, wasu na alaƙanta hakan da rashin rungumar sana’a da galibin matasan suke yi. Sai dai masu iya magana kan ce: ‘Allah ɗaya, gari bam-bam’. Domin kuwa, Jamilu Abubakar Isa matashi ne kuma ɗan boko dake cikin jerin masu cin duniyarsu bisa tsinke a ɓangare dogaro da kai, bayan da ya yi wa kansa karatun ta-natsu tun yana ƙanƙani kan rungumar sana’oi daban-daban, domin kawai ya dogara da kansa. Wakilin Blueprint Manhaja a Sokoto Aminu Amanawa, ya zanta da shi inda ya bayyana wa masu karatu irin gwagwarmayar da ya sha a rayuwa wajen neman halak malak, nasarori da ƙalubalen da ya fuskanta, da ma shawarar da ya bawa ‘yan uwansa matasa na irin matakan da yake tunani idan matasa suka taka, to tabbas haƙar su za ta kai ga cimma ruwa. Ga yanda yanda tattaunawar tasu ta kasance:

BLUEPRINT MANHAJA: Da farko ka gabatar da kanka.
JAMILU: Sunana Jamilu Abubakar Isa, wasu suna cewa Honarabul Jamilu Abubakar Isa. Kuma ni ɗan asalin ƙaramar hukumar Isa ne ta jihar Sakkwato. A nan na girma, a nan na yi firamare ɗina, a nan na yi karatun sakandare ɗina a makarantar gwamnatin je-ka-ka -dawo ta Isa, wato GDSS Isa. Daga nan Allah cikin ikonsa na je kwalejin kimiyya da fasaha ta Umaru Ali Shinkafi Polytachnic ta yanzu, a lokacin tana ‘Sokoto State Polytechnic’.

A nan na karanci ɓangaren sashen jarida wato ‘Mass Communication’ kenan, a Turance. Na yi Diploma a lokacin a ɓangaren koyarwa. A halin yanzu ni ɗalibin ne a jami’ar jihar Sakkwato, ina kan ƙarewa kafin soma yajin aikin nan na ASUU da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa, inda nake nazartar sashen ilimin sanin halayyar ɗan Adam wato ‘Sociology’ a Turance.

Na’am, mun ji ta ɓangaren karatu, kowa ya san Jamilu Abubakar ya yi fice a kan abinda ya shafi sana’o’in dogaro da kai a Sokoto. Ya aka yi ka tsinci kanka ta ɓullowa da sana’o’in dogaro da kai a lokacin da matasa suke ƙorafin ba su da ayyukan yi?
To ka san shi abinci ana neman shi kafin a ji yunwa, duk wanda ya nemi abinci bayan ya ji yunwa, to dole akwai wani sakamako. To tun tashi na dai gaskiya na bawa kaina shawarar ya kamata a ce na taimaki kaina. Tun ina zuwa firamare idan an bani kuɗin tara rage su nake yi in ajje in tara, idan sun kai Naira 200, 300, in siyo katako, in ɗan siyo ‘yar ƙusa ta Naira 50 haka in harhaɗa kujeru irin ƙananan nan irin na zaman tsakar gida haka. Can gida ƙauye ina siyar da kujera Naira 120 mai saidawa, yaron dake shiga cikin gida shike da Naira 20. Ni ke da Naira 100.

Haka nan har na zo na ɗan yi ‘yar tireda haka na zo ana kawomin sandunan rake na zo ina yankawa, ina saidawa. haka nan dai da ta faru ta ƙare na kammala makarantar Sakandare, sai na zo na ga kai! ya kamata a ce na shiga Duniya saboda arziki na can cikin Duniya da yawa.

Saboda haka, farko na fara sana’ar waƙa. Na haɗu da wani maigidana ana ce masa Abubakar Tsoho nan cikin garin Katsina, na koyi harkar waƙa. Kafin na bar harkar waƙa, na yi waƙoƙin da suka kai guda 100 haka, insha’Allah.

Za a iya cewa kai mawaƙi ne?
Eh na yi waƙa a da.

To ka daina waƙar ne yanzu?
Eh, to. Zan iya cewa na bari, ko ban bari ba. Yanzu ma idan aka buƙace ni zan yi. Amma mafi yawanci al’adar waƙa idan baka yi fice ɗin nan ba, ba za a iya baka abin kirki ba, idan ka yi waka. Ni kuma ainahin basirata ba alfahari ba da fasahata, in bazzarar da basirata haka nan ba wani abun ƙwarai, to shi ya sa za ka iya ganin kamar za mu yi shekara ɗaya, shakara biyu, ban yi waƙa ba.

Ka fi son sha yanzu, magani yanzu kenan?
Ba maganar sha yanzu, magani yanzu ba. Ai an yi waƙoƙin. Na ce maka na yi sun fi 100. Akwai waƙoƙin da muka yi na mutane sun fi mutum saba’in zuwa tamanin.

Yanzu wacce harkar ake yi?
A yanzu haka, na tsinci kaina cikin harkar ɗab’i. A lokacin da na ga harkar waƙa tana ƙoƙarin kifewa dai da ni, abubuwan kamar dai ana son a daina yi da mu ko kuma ba mu samun biyan buƙata dai yadda ya kamata. Sai na zo na haɗu da wani maigidana wanda ke da Maimagi Dub Studio, wato Oga Sani Maimagi yana zaune Kaduna. Na ce, Oga ka taimake ni.

Ya ce da me Honarabul? Na ce ka taimaka min Oga ka a sa ni bisa ga hanyar sana’a, ka ga yadda al’ummarra suka kasance. Sai a ka yi ta dariya, daga baya dai sai ya ce min, “babu matsala insha’Allahu” To haka ya bi da ni a wurinsa na koyi aikin ɗab’i, na kafa sana’ar harkar ɗaukar hoto da ɗab’i, lokacin bani da kayan aiki, arowa nake yi. Na gina shago 17 to 18, kasuwancin ya ruguje saboda babu jari, babu kayan aiki.

Daga baya dai abin ya farfaɗo a 2019, na fara azawa. To kawo yanzu dai gaskiya Alhamdulillah, mun kafa kamfanoni biyu; akwai Jamil Print Production and general enterprises, wanda muka yi wa rajista da CAC, muka sami satifiket da sauran ƙa’idoji muka cika a 2019.

Akwai kuma J I Communication and Broadcasting wanda muka yi wa rijista a 2021, sai kuma wannan na Jamil Film Production Enterprises, da ɗab’i da ɗaukar hoto da sauransu. A kamfanin mu na J.I Communication muna yin Jingle da sa, wannan dai a bisa abinda mu ke yi kenan.

Na’am, to da yake kana da hanyar dogaro da kai, kuma wannan sana’ar ta ɗab’i, sana’a ce da qila ba za ta yiwu ba mutum ya yi ta shi kaɗai ba, kamar akwai mutane nawa waɗanda suke ci a ƙarƙashinka?
Eh to, a zahirance yanzu muna da kusan mutum goma waɗanda muke mu’amala da su; akwai waɗanda suke zaune, muke zaune, ka gani za su kai mutum huɗu biyar muna tare da su. Akwai kuma mutum sun kai biyar waɗanda su ba a nan suke ciki ba.

Kamar akwai Abubakar wanda ya ke sashen ɗaukar hoto, sai ayukka sun samu za a kira shi ya zo ya ɗauki kayan aiki, akwai kuma manajanmu na kula da jama’a wanda ba a nan yake zaune ba, akwai kuma mai kula da shirye-shirye wanda zuwa yake ya ga yadda al’ummarra suke tafiya da dai sauransu. Ka ga aƙalla za mu iya cewa mutum kusan goma suna cin abinci ciki, har ma da ni mai magana. Da shi nake ci, da shi na ke sha, da shi nake sutura.

Wacce irin nasara ce wannan dogaro da kai ya samar maka?
Malam Aminu ai duk wanda ya ga Jamilu shekarun da suka wuce, ya ga Jamilu yanzu ya san an ci nasara Alhamdulillah! Dai-dai lokacin da ake ta kuka ana cewa Nijeriya ta rikice, idan ka lura, mai sana’a a wannan lokacin to wallahi shike da nasara. To wallahi duk wanda ya tsaya ga aikin gwamnati ba sana’a, ai yanzu suna nan suna karɓar kiɗin janaral, saboda rayuwa ta yi tsada ko nawa ka ke karba na albashi ya zamo alwashi.

Da zaran kuɗin sun shigo, za a je a yo cefane ga magidanta kenan. Matasanmu a na nan, ana gararamba a gari, babu aikin yi. Ni kam Alhamdulillah na ci nasarori da yawa, domin kuwa ina taimakon Mahaifiyata da ƙannena , kuma duk a cikin wannan sana’ar. Insha’Allah muna nan muna neman iyali da za mu zauna da su in Allah ya ce.

Me kasa a gaba yanzu?
A ɓangaren sana’a gaskiya ina da babban buri. Burina wannan kamfanin na farko Jamil Print Production Enterprises, manhajar tsarin kasuwancinmu ma in ka duba, zan ɗauko maka ka duba ka gani. Muna da motoci sun kai wurin guda bakwai ko wacce da aikinta, muna da na’urori waɗanda muke so mu saya waɗanda za su iya kai wa miliyan ɗari, wanda ba mu da isasshen jarin da ya kai miliyan uku a ƙasa yanzu. Saboda haka, abubuwan da muka sa a gaba suna da yawa.

A cikin manhajar tsarin kasuwancinmu akwai motocin da za mu yi aiki da su na kai saƙo, akwai na tallace-tallace, akwai na’urorin da muka rubuta waɗanda kowanne da yanayin da za su ba da. Mun yi manhajar tsarin kasuwancin ma wanda har da gini da muke son mu yi, ballanta mu zo wurin babban Companyn da mu ke kirkira yanzu.

Menene shawararka daga ƙarshe ga matasa masu tasowa ta yadda za su dogara da kai?
To ai Malam Aminu yanzu ba a buƙatar shawara. Ai shawara a fili ta ke, ba sai an ce maka ka dogara da kanka ba, kai kanka kasan ya kamata a ce ka dogara da kanka. Bari na gaya maka Malam Aminu, ko da na tashi a cikin gidanmu na gado, gidan laka da na tashi.

Jamilu Abubakar a bakin aiki

Akwai ɗan aikin gidanmu da zai hau babur ya je ko’ina da shi, kai har mota na san ya tava ɗauka ya buga ta wani wuri, kuma ya dawo ba wanda ya ce mai ko ƙala. Amma wallahi ban tava hawa ko motar gidanmu ba na yi tafiyar ko daƙiƙa ɗaya da ita ba. Har zuwa yanzu, ban tava taka motar gidanmu na yi tafiyar Naira biyu da ita ba.

Ba za a baka ba ne?
Ba zan hau ba dai! Aƙidata ce. Burina ni na ga na mallaki nawa na kaina, duk lokacin da za a yi tafiya gidanmu ta kowa, ni tasha nake zuwa in shiga mota in yi tafiya ta. Ban taɓa shiga motar gidansu ba, in riga su da kwana guda kuma sai sun dawo da kwana guda in shigo ta kasuwa in dawo in biyo su, saboda me?

Ina son in tabbatar da cewa ni zan iya tsayuwa da kaina! A kan haka nake ba matasa shawara, babu lokacin da zan zauna in faɗi tarihin rayuwata daga farko ƙar na ƙarshe. Amma Malam Aminu, mun tava hira da kai na gaya maka cewa, na yi na kwando, na yi turin baro, na yi kwasar bola na yi ban ruwan fulawoyi, akwai lokacin da ta ke kwalewa ma babu na kwandon babu turin baron babu kwasar bola babu ban ruwan. Muna garin Kaduna za mu je mu ɗauki roba mu yi bara. Sai an zo ana ina almajirin, mu miqa roba, a zubo mana abinci mu laƙume.

Don haka, abinda nake so na kira matasa a matsayinka na matashi ko meye za ka iya zama, tunda nake, ban tava sa ran zan ga wani matashi ba wanda ya kai ni domin ina da burin da za a kwatanta Ni da aliko Ɗangote. Da dubu ɗaya da ɗari biyar Malam Aminu za ka iya zama miloniya. Duk matashin da ke neman zama miloniya da N1,500, ya neme ni, ni Jamilu Abubakar zan bashi dabarar yadda zai zama biloniya da Naira 1500, ni na faɗi wannan.

Muna godiya
Ni ma na gode Malam Aminu!