Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A ranar Larabar da ta gabata, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyae NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fuskanci famakin siyasa da wasu ’yan bangar siyasa a Jihar Kogi, inda suka yi masa a-ture a lokacin yaƙin neman zaɓen da ya gudanar a jihar.
Majiyar gani da ido ta ce, a yayin da ɗan takarar ya iso wani otel da nufin gabatar da jawabi ga tsirarun magoyansa ne, sai matasan suka suka shiga yi masa ihu tare da jifan su da ruwan leda har ma da duwatsu.
Sai da jami’an tsaron da ke tare da tsohon sanatan suka hayayyaƙo wa matasan ne ƙurar ta lafa.
Tun da fari dai, Kwankwaso ya ziyarci Ogbonicha, wato mahaifar tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Marigayi Prince Abubakar Audu, inda nan ma aka samu wasu matasa suka yi masa ihu, suna masu zargin sa da ƙoƙarin yin amfani da sunan marigayin wajen janye magoya bayan Jam’iyyar APC mai mulkin jihar, lamarin da ya kai ga hana Kwankwaso sakat a duk inda ya je yaƙin neman zave a jihar.
