JAMB: Kaso 75 na ɗaliban UTME ba su samu maki 200 ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar haɗaka da ke kula da bada gurbin karatu ga ɗalibai, JAMB, ta fitar da cikakken sakamakon jarrabawar UTME da ɗaliban sahun 2025 suka rubuta.

Ta kuma yi bayani dalla-dalla kan yadda ɗaliban suka rubuta jarrabawar da yadda sakamakon nasu suka kasance.

Ɗalibai da iyaye da dama sun koka game da matsalolin da aka samu daga UTME, wanda aka fara a ranar Alhamis, 24 ga watan Afrilu.

An samu rahotannin matsalolin netwok da na gudanarwa daga cibiyoyin kwamfuta na JAMB, wato ‘CBT centres’ da suka haɗa da jinkiri da rashin samar da damar rubuta jarrabawar ga wasu ɗalibai.

Ga bayanin yadda sakamakon ya kasance kamar yadda Blueprint ta ruwaito; “According to JAMB official figures, a total of 1,955,069 candidates sat for the UTME, with performance across score ranges as follows: 320 and above (4,756 or 0.24 percent), 300–319 (7,658 or 0.39 percent), 300 and above (12,414 or 0.63 percent), 250–299 (73,441 or 3.76 percent), 200–249 (334,560 or 17.11 percent).”

“The candidates who scored 160–199 are 983,187 or 50.29 percent; 140–159 (488,197 or 24.97 percent); 120–139 (57,419 or 2.94 percent), 100–119 (3,820 or 0.20 percent, while those who scored below 100 are 2,031 or 0.10 percent.”

Ɗaliban da dama sun koka kan yadda suka rubuta darussan lissafi, Fiziks da kwamas cikin yanayi na ƙalubale musamman ganin yadda suka saɓa da rubutuwa a takarda, inda kuma a ɓangaren darasin turanci, wato ‘Use of English’ suka samu sauƙi.

Wasu daga cikin ɗaliban sun ce, wasu tambayoyin sun ɓace a na’urorin yayin da amsoshin zaɓinsu kuma suna nan.

Wasu kuwa ƙin tantance su kwamfutocin suka yi a yayin fara rubuta jarrabawar, wanda ya ba su samu damar rubutawa ba.

Lamarin da ya sa JAMB ta ƙaddamar da bincike akan dalilin rashin tantancewar, inda ta ce za a bai wa waɗanda aka tabbatar da gaskiyar lamarin akansu damar sake rubutawa.

Bugu da ƙari, ta ce za a fitar da sakamakon ɗalibai makafi nan ba da jimawa ba ganin cewa har yanzu ba a kammala aikin nasu ba.

By Babaji