JAMB za ta kafa cibiyar rubuta jarrabawar UTME a ƙasar Canada a 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Nijeriya (JAMB) ta ce tana shirin kafa cibiyar gudanar da jarabawar shiga jami’a ta UTME a Ottawa da ke ƙasar Kanada, wadda ake sa zai fara aiki a shekarar 2027.

JAMB ta ce cibiyar za ta bai wa ‘yan Nijeriya da ke zaune a Kanada da sauran sassan Arewacin Amurka damar rubuta jarabawar UTME ba tare da sun dawo domin rubuta jarabawar ba.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na ɗ a ranar Litinin.

Ta ce shirin zai ƙara damar samun ilimi tare da rage ƙalubalen da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke fuskanta wajen neman gurbin karatu a manyan makarantun Nijeriya.

Sanarwar ta biyo bayan ziyarar da shugaban JAMB, Segun Aina, ya kai ofishin Babban Jakadancin Nijeriya da ke Ottawa, inda aka tattauna batun kafa cibiyar.

“Cibiyar da aka shirya za ta sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya da suka cancanta da ke Kanada da sauran sassan Arewacin Amurka rubuta UTME ba tare da sun yi tafiya zuwa Nijeriya musamman domin jarabawar ba,” inji JAMB.

Hukumar ta ƙara da cewa cibiyar za ta kasance wata dama ta ƙarfafa alaƙar ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje da tsarin ilimin manyan makarantu na Nijeriya.

‘Yan takarar da ke neman shiga manyan makarantun Nijeriya dole ne su rubuta UTME kafin su shiga matakin neman gurbin karatu a makarantun da suka zaɓa.

Jarabawar na samun miliyoyin ɗalibai kowacce shekara kuma fiye da ‘yan ɗalibai miliyan biyu ne suka rubuta UTME a bana.

JAMB ta riga tana gudanar da UTME a wasu ƙasashen ƙetare ciki har da Birtaniya, Ghana, Afirka ta Kudu, Saudiyya da Kwadebuwa.

A tsarin karɓar ɗalibai na shekarar karatu ta 2026/2027, JAMB da sauran masu ruwa da tsaki sun amince da maki 150 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga jami’a.

An kuma ƙayyade maki 100 a matsayin mafi ƙarancin maki na shiga kwalejojin fasaha, kwalejojin ilimi, kwalejojin aikin gona da sauran manyan makarantun da ke ƙarƙashin wannan rukuni.

By ukarofi

Leave a Reply