Jami’an KAROTA sun cafke direban Adaidaita Sahu ɗan damfara a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano KAROTA, ta ce ta cafke wani magidanci ɗan damfara bayan ya damfari wata kuɗi har Naira 600.000

Hakan na ƙunshe ne ta wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Malam Nabulusi Abubakar Ƙofar Na’isa ya fitar a daren Talata da ta gabata.

Sanarwar ta ce, jami’an hukumar ta KAROTA, sun sami nasarar kama magidancin ne mai suna John Bandes a kan titin Obasanjo da ke cikin birnin Kano.

“A makon da ya gabata ne wata budurwa mai suna Jenifer Paul ta shigar da ƙorafi a Hukumar KAROTA bayan damfarar da magidancin ya yi mata ta hanyar amfani da babur ɗin Adaidaita Sahu,” inji sanarwar.

Haka kuma Nabilusi a sanarwar ya ƙara da cewa, Jenifer ta shaida wa hukumar cewa lokacin da ta hau Adaidaita Sahun watanni biyu da suka gabata, magidancin ya damfareta zunzurutun kuɗi har Naira dubu ɗari shida.

An samu nasarar cafke Adaidaita Sahun mai lambar RRN 231QA da kuma Koriyar lambar FGE 19-0849.

Magidancin mai suna John Bandes ɗan kimanin shekaru 45 ya bayyana wa Humar KAROTA ba shi kaɗai yake aikata damfarar ba suna da yawa, kuma sun shafe fiye da wata shida suna damfarar jama’a a nan Kano da babban birnin tarayyar Abuja.

“A binciken da hukumar KAROTA ta gudanar ta gano yadda John ke amfani da wani sinadari a cikin wata kwalba, da zarar sun zuba wa fasinja zai samu juyewar kai, sai yadda suka yi da shi kamar yadda Jenifer ta bayyana,” a cewar sanarwar.

Haka kuma ya ce, KAROTA ta gano cewa John ya jima yana aikata saqa da mugun zare kafin dubunsu ta cika.

“Wani binciken sirri da KAROTA ta samu ya bayyana cewa fiye da watanni shida da suka gabata rundunar ‘yan sanda ta baza koma wajen ganin an damƙe John ɗin sai a wannan rana dubunsu ta cika,” inji jami’in.

Sanarwar ta hukumar KAROTA ta kuma ce, hukumar ta miqa John ga Baturen ‘yan sanda na Badawa domin faɗaɗa bincike tare da ɗaukar mataki na gaba a kansa.

Haka zalika kukumar KAROTA ta ja hankalin jama’a da su ci gaba da sanya ido a kan duk wani matuƙin Adaidaita Sahu kafin su hau domin gujewa faɗawa hannun ɓata-gari.