Salah ya kafa tarihin zura ƙwallaye uku cikin sauri a gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Liverpool Mohamed Salah ya kafa tarihin shiga sahun waɗanda suka yi nasarar cin ƙwallaye 3 a wasa guda cikin sauri a gasar kofin zakarun Turai, bayan da ya zura ƙwallayen 3 wato ‘hattrick’ cikin mintuna 6 da shiga fili a karawarsu da Rangers daren Laraba.

Ƙwallayen na Salah dai ya goge tarihin Bafetimbo Gomis na Lyon wanda ya taɓa nasarar zuwa ƙwallaye 3 cikin mintuna 8 yayin wasansu da Dinamo Zagreb a 2011 ƙarƙashin makamanciyar gasar

Yayin wasan na daren Laraba da ya gudana a Ibrox Liverpool ta tashi wasa 7 da 1 ne tsakaninta da Rangers har gidanta kuma shi ne wasa na farko a cikin kakar nan da aka ga ’yan wasan Liverpool na nuna bajinta irin wannan.

Har zuwa yanzu dai wasanni 4 kacal cikin 11 da Liverpool ta doka ne ta samu nasara, musamman a gasar firimiyar Ingila da yanzu haka ƙungiyar ke matsayin ta 10 da maki 10, dalilin da ke ci gaba da janyowa ’yan wasan kakkausar suka daga magoya baya.

Sai dai duk da nasarar ta Liverpool ƙungiyar ta cigaba da zama ta 2 a rukuninta, yayin da ta ke buƙatar aƙalla canjaras da Ajax gabanin iya tsallakawa rukuni na gaba.