‘Yan sandan Jihar Kano sun yi ram da matashin da ya hallaka abokinsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Ibrahim Khalil da ke Unguwar Ƙofar Mazugal cikin Ƙaramar Hukumar Dala a birnin Kano.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan yayin zantawarsa da manema labarai a Talatar da ta gabata a Kano.

SP Kiyawa ya ce, lamarin ya faru ne sakamakon samun wani rashin jituwa tsakanin marigayin da wani mai suna Salisu Bala ɗan kimanin shekaru 18.

Wanda ya bugi Ibrahim har ya kai ga ya rasa ransa kamar yadda SP Abdullahi Haruna kiyawa ya bayyana.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar damƙe wanann matashi da ya aikata laifin domin gurfanar da shi a gaban kotu.