Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’an Hukumar Kula Da Dokokin Hanya ta Jihar Katsina, wacce aka fi sani da KASROTA, sun ci zarafin wakilin Blueprint Manhaja a Katsina, Umar Garba, lamarin da ya kai ga ƙwace kayan aikinsa da suka haɗa da na’urar naɗar murya, wayoyin salula da kuma abun hawansa.
Lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata a hanyar ƙofar Durɓi zuwa G.R.A, inda jami’an Kasrotar suka saka shinge, don tsayar da masu ababen hawa. A nan ne ɗaya daga cikinsu da ake kira ‘Arewa’ ya tsayar da ɗan jarida, Umar Garba, a yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa aiki.
Jami’an sun buƙaci ɗan jaridar ya ba su takardun lambar babur ɗinsa, sai dai ya faɗa ma su cewar, bai fito da takardun ba, amma ya nemi su ba shi mintuna, don a kawo masa takardun wajen da suke aikin.
“Na faɗa masu ban fito da takardun lambar ba, amma su ba ni mintuna 15 kacal, don na kira waya a kawo min takardun, amma suka ƙi amincewa,” inji Umar Garba.
“Nan take ɗaya daga cikin jami’an na Kasrota ya buƙaci na bayar da cin hancin Naira 5,000, don a sakar min babur ɗina da suka ƙwace, amma na ce ni ba zan bayar da ko sisi ba, saboda ban aikata wani laifi ba duba da cewa takardun da suka buƙata Ina da su kuma sababbi ne,” Inji shi.
Sai dai ko da ɗan jaridar ya lura cin hanci kawai jami’an ke buƙata daga wajensa, sai ya yi amfani da wayarsa, inda ya fara naɗar muryar ɗaya daga cikinsu mai suna Oga Arewa, wanda ke karɓar Naira 5,000 ga masu ababen hawan da aka kama a lokacin.
“Na fara naɗar muryarsa a asirce lokacin da ya dage sai na bayar da kuɗi kafin su ba ni kayan aikina, ashe wani abokin aikinsa ya lura ‘recording’ na ke yi, shine ya zo kusa da ogan nasu ya raɗa masa a kunne cewar, ‘Oga ana ɗaukar maganarka saboda haka ka ƙyale shi ya tafi kawai’.” Inji Umar.
Sai dai naɗar muryar jami’in Kasrotar da ɗan jaridar ke yi lokacin da ya nemi a ba shi cin hanci bai yi ma sa daɗi ba, domin kuwa sai ya ƙwace wayar daga hannunsa ya kuma goge muryar da ɗan jaridar ya naɗa.
“Daga ƙarshe bayan cin mutunci da ɓata min lokaci da jami’an Kasrotar suka yi, sun ba ni babur ɗin da sauran kayan aikina da suka ƙwace, don gudun kada na fallasa su,” inji ɗan jaridar.
Da ma dai al’ummar Jihar Katsina, musamman masu ababen hawa, sun daɗe suna zargin jami’an kula da dokokin hanyar da rashin iya gudanar da aiki, haddasa haɗɗura akan hanyoyi, dambacewa tsakaninsu da direbobi da kuma karɓar cin hanci daga wajen masu ababen hawa.
Blueprint Manhaja ta tuntuɓi Kakakin Hukumar ta KASTORA, Malam Abubakar Marwana, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa tare da jajenta wa ɗan jaridar game da faruwar lamarin. Sai dai bai bayyana ko hukumar ta Kasrota za ta ɗauki wani mataki ba kan jami’an nata, waɗanda al’ummar jihar suka daɗe suna zargi bisa aikata irin waɗannan laifuka, ko kuma akasin hakan ba.
