Daga USMAN KAROFI a Abuja
Jami’an lafiya a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa sun sami nasarar duba mata da ƙananan yara guda 67,262 a lokacin gudanar da makon mata da ƙananan yara da aka yi a yankin. Wannan bayanin ya fito ne daga shugabar sashen lafiyar matakin farko na yankin, Hajiya Balaraba B. Gambo, a wata hira da jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar.
Hajiya Balaraba, ta bakin wakiliyarta Hajiya Talatu Sale, jami’ar kula da lafiyar mata da ƙananan yara, ta ce cikin waɗanda suka amfana akwai mata masu juna biyu 372 da aka basu magunguna, ƙananan yara 58,316 da kuma wasu yara 8,574 da suka samu kulawar lafiya cikin shirin. Ta ce an shafe kwanaki biyar ana gudanar da wannan aiki, kuma a halin yanzu ana jiran cikakken rahoton yawan waɗanda suka amfana gaba ɗaya.
A cikin shirin, yara ƙanana sun samu sinadarin Vitamin A da magungunan tsutsar ciki, yayin da mata masu juna biyu suka samu maganin ƙara jini da sauran kariyar lafiya. Hajiya Balaraba ta nuna farin cikinta bisa nasarar da aka samu, tare da jinjinawa al’ummar Dawakin Tofa bisa haɗin kai da goyon bayan da suka bayar. Ta kuma yaba wa shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Anas Mukhtar Bello Ɗanmaliki, bisa irin kulawa da goyon bayan da yake bai wa fannin lafiya a yankin.
