Daga USMAN KAROFI a Abuja
Kwamishinan sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa jim kaɗan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Ɗanwawu. Wannan matakin ya kasance wani ɓangare na jajircewar gwamnatin jihar wajen tabbatar da gaskiya, adalci da ɗorewar amana a tsakanin jami’an gwamnati.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Namadi ya ce ya yanke shawarar sauka daga muƙamin sa ne domin kare mutuncin gwamnati da kuma ɗaukar alhakin shugabanci.
Ya ƙara da cewa: “Ko da yake ina da tabbacin cewa ban aikata wani laifi ba, ba zan iya watsi da ra’ayin jama’a ba, kuma ina da burin kare ƙimar da muka gina tare da wannan gwamnati.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin girmamawa tare da fatan alheri ga tsohon kwamishinan a harkokinsa na gaba.
Ya kuma sake jaddada manufar gwamnatinsa na yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ɗabi’un da ke lalata matasa, tare da shawartar sauran masu riƙe da muƙamai su kasance masu taka-tsantsan a harkokin da suka shafi al’umma.
