Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliero ta buɗe reshe a garin Koko

Spread the love

Daga JAMIL GUlLMA a Kebbi

Jami’ar kimiyya da fasaha mallakar jihar Kebbi da ke garin Aliero (Abdullahi Fodio Universiry of Science and Technology, Aliero), ɗaya daga cikin jami’oin da ke faɗin Nijeriya ta buɗe reshe a garin Koko don sauƙaƙawa ga masu sha’awar karatun diploma a fannoni daban-daban.

Aliyu A Haliru jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar cigaban ƙasar Koko ya bayyana cewa kamar yadda ake gabatar da karatun digiri ana karatun diploma a jami’ar.

Ganin hakane yasa ƙungiyar cigaban matasan Koko da kewaye KOYDA ta yi hoɓɓasa wajen haɗin gwiwa da Jami’ar Abdullahi Fodio don kawo karatukan diploma a garin Koko kafin na digiri in sha Allah domin sauƙaƙawa ɗalibai shiga jami’a cikin sauƙi ba tare da wahala ba.

Wannan sauƙi ne da ƙungiyar KOYDA ta samar wa matasan yankin na Koko da kewaye. Sassan diploma da aka kawo a garin Koko sun haɗa da karatun kimiyyar na’ura mai ƙwaƙwalwa, gwaje-gwajen lafiya, lafiyar dabbobi, aikin lantarki da kuma ɗakunan bincike.

By ukarofi

Leave a Reply