Daga BASHIR ISAH
Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta ƙasa, Farfesa Stella Effah-Attoe, ta rasu.
A cewar ahalin marigayiya, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da rashin lafiya.
Cikin sanarwar da ta fitar ta bakin sakataren hulɗa da jama’a na ƙasa, Debo Ologunagba a ranar Lahadi, PDP ta bayyana rasuwar Effah-Attoe a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya.
Sanarwar ta ce a halin rayuwarta, Farfesa Effah-Attoe ta kasance mai himma da ƙwazo wadda ta bada gudummawarta ga cigaban jama’a da ma ƙasa baki ɗaya.
Ologunagba ya ƙara da cewa, rasuwar Effah-Attoe ta bar wagegen giɓi a jam’iyyar PDP, kuma Jam’iyyar ba za ta taɓa mancewa da gagarumar gudummawar da ta ba ta ba.
