Makamashi: Duniya labari

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASI

“Duniya Labari,” inji masu hikimar zance. Falsafar wannan magana tana tasowa ne ‘yayin da wani abu na son zuciya ya fito muraran, sai ka ji an furta wannan kalami, domin tunasarwa cewa wannan al’amari ba sabon abu ba ne, domin ya taba faruwa a wani lokaci baya.

Saboda haka za mu yi waiwaye kamar yadda masu nazarce-nazarce ke cewa, “adon tafiya”. Duniya ta sami kanta cikin mawuyacin hali na buƙatar makamashi, saboda yawaitar masana’antu a faɗin duniya. Kowacce ƙasa na fafutukar samar da masana’antu domin samar da ababen buƙata ga ‘yan ƙasarta da sauran al’ummar duniya, wanda daga ƙarshe za ta samu kuɗaɗen shiga ƙasarta.

Daga 1950 zuwa 1960, duniya bakiɗayanta ta bazama wajan neman makamashin man fetur da dangoginsa, kamar gas, saboda dafe-dafe da girke-girke da kuma ɗumama mahalli. Wannan shi ya haifar da ƙungiyar masu haƙo man fetur da dangoginsa da kuma kai su ƙasashen waje, domin sayarwa. Ƙasashe biya; Iran da Iraq da Kuwait da Saudi Arabia da kuma Venezuela su suka kafa wannan ƙungiya da suka kira OPEC a taƙaice a watan satumba na shekara ta 1960.

Saboda haka kafin shekara ta 1970, ƙasashe sama da 22 sun zama mambobi a cikin wannan ƙungiya a ciki har da ƙasashen nahiyar Afrika kamar Nijeriya da Algeriya da Angola da Ekotoriyal Guini da Gabon da Libiya da kuma Jamhuriyar Kwango.

Abin baƙin ciki ƙasar da sauran ƙasashen Turai, wato ƙasar Birtaniya da Faransa da Portugal da Jamus da wasu ‘yan kanzaginsu sun karɓe wannan ƙungiya ta OPEC, sai yadda suka dama za a tafiyar da ƙungiyar wajen ganga nawa ya kamata a haƙo a kullum kuma farashi nawa za a siyar a duniya kuma da wannan kuɗi za a siyar a duniya kuma da wannan kuɗi za a yi amfani da shi wajen cinikin wannan makamashi da duniya take buƙata.

Wannan ya sa ƙasashe irin su Ecuador da Indonesia da Qatar suka fice daga cikin wannan qungiya ta OPEC. Ganin yadda ake dukan jaki ake barin taiki, kuma gardi da karvar kuɗi, a shekara ta 2016 aka kafa kishiyar OPEC, wato “Non- OPEC Countries” ta waɗanda su za su yanke farashi da kuma ƙasashen da za su sayarwa. Waɗannan ƙasashe su ne Azerbaijan da Behrain da Brunei da Kazakhistan da Malaysia da Mexico da Oman da Russia da Sudan ta Kudu da kuma Sudan ta Arewa.

Duniya Labari, kullum talaka bawan Allah shi ne a ƙasa, shi ake yi wa sukuwar sallah akansa, an yi amfani da noma da kiwo inda aka riƙa kwasar bayi a wannan nahiya ta Afirka ana kai su Amurka ta Arewa, wato USA da ta Tsakiya irin su Brazil fa French Guiana da Suriname da Guyana da Venezuela da Colombia da Panama da Costa Rica da Nicaragua da kuma Honduras. Bayan an gama da harkar noma da kiwo aka koma ma’adainai da kuma masana’antu, a nan ma nahiyar Afirka ita aka riƙa wawaso a cikinta.

Kowa ya san yadda waɗannan qasashe na yammacin Turai suka mamaye nahiyar Afirka suka yi musu mulkin mallaka na sama da shekara 60 daga 1900 zuwa 1960 a lokacin da suka fara ba su ‘yancin je-ka-na-yi-ka, wato a na murna baƙo ya tafi, ashe yana bayan gari. Sun kwashi ma’adanai irin tama da baƙin ƙarfe da gorar ruwa da lu’u-Lu’u da zinare da azurfa da makamashin kwal (Coal) da yureniyum (Uranium), yanzu kuma suna kwasar man fetur da gas (Oil and Natural Gas).

Ɗan uwana mai karatu duk faɗin duniyan nan, idan ka ji ana wai-wai kuma ana gutsiri tsoma, magana ce ta makamashi na tafashasshen ruwa (Thermal energy) ko haɗe-haɗen wasu sinadarai, wanda zai bayar da wani ƙyastu, kamar na ashana ko alburushi wanda suke kira ‘Chemical energy’ ko daga haske, wato ‘Radiant energy,’ ga kuma makamashin nukiliya (Nuclear energy) ga na wutar lentarki (Electrical energy).

Baya ga haka ga makamashi da ake samarwa da sinadarin motsi (motion) da sinadarin amo ko amsa-kuwwa, kamar yadda ruwan kogi ya ke gangarowa daga kan tsaunika ko duwatsu, suna kiran tsarin da ‘gravitational force,’ nan da nan sai a smar da makamashi da shi, kamar Kayinji da Shiroro da kuma Jibba dukkansu a Jihar Nijar a wannan ƙasa ta Nijeriya.

Duk ƙasar da Allah ya hore mata ma’adanai da makamashi da ambata a sama wannan ƙasa ta shiga uku kuma ta lalace, domin waɗancan ƙasashe da ake kira “Kasashe masu ringingimu a tsakanin ‘yan ƙasa ta fuskar qabilanci ko riqa amfani da aƙidar dimukraɗiyya, wato ’yancin faɗi, na faɗa da kuma ‘yancin kafa ƙungiyoyin siyasa kamar yadda muke gani a Nijeriya. Baya ga haka sai waɗannan ƙungiyoyi na siyasa su rarraba ‘ya’ya da iyayen su raba mata da maza, wa da ƙani, maƙoci ana gabar aƙidar siyasa.

Waɗannan ƙasashe na yammacin Turai da Amurka su na yin amfani da wannan tsari na dimukraɗiyya wajen rarraba kawuna, domin su sami damar kwasar waɗannan ma’adanai da makamashin man fetur da dangoginsa ta cire aƙidar gaskiya da amana da karamci da haƙuri da hankali da kunya da ladabi da mutunci da hikima da kuma adalci a zukatan al’umma. Wannan shi ya haifar da aƙidar tara abin duniya ta kowanne hali. Aka cire tausayi a kowanne mataki.

Wannan shi ne musabbabin fitowar cin hanci da rashawa da dukiyar ƙasa ta zama ta mutum ba kunya ba tsoran Allah balle za ka ga lauyoyi na ta waɗari a kotuna domin sun san ga nama ya faɗi sai shi kuma gobe ku hadu da shi a wajen bikin ‘ya’yansu da suka haɗu a dandalin sada zumunta na ‘Tie-Talk,’ inda za a yi sati (mako) ana raƙashewa da mawaƙan zamani na nanaye.

Daga ƙarshe sai ka ji an ce wai EFCC ko ICPC ko kuma SSS sun kasa tabbatar da laifin wannan mutum, don haka ya kwashi rabonsa.

Shi ya sa za ka ga matasa na ta kokawar shiga wadannan hakumomi daga NNPC sai su, ba don komai ba cikin ƙanƙanin lokaci ka zama oga a ƙauyenku nan da nan sai ka ji ana kiran sa da Bala “Toshe Hanci”, haka zaka ta jin suna yana fitowa daga ƙauyuka wai kakan kakansa shi ya auri mai wa matar dagacinsu kitso a lokacin suna shi ya auri mai wa matar dagacinsu kitso a lokacin suna raye. Saboda haka tunda shi wannan sarauta a gurinsu.

Kamar kyautar matsayin dokta da jami’oi ke bayar a wannan lokaci shi ya sa za ka ji sunansa na haƙiƙa za ka ji ana Dokta Madugawa Dokta Obizor ko kuma Dokta Olusola da dai sauransu.

Mu haɗu a makon gobe da yardar Allah!

By Editor