Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Masarautar Kabin Argungu da ke jihar Kebbi ta ɗaura ɗamarar yaƙi da masu tauye ma’auni kan harkokin sayar da abinci a kasuwanni da ke yankin wannan masarautar.
Alhaji Abubakar Yaya shi ne Sarkin Bakin Kabi kuma shugaban gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin ladabtarwa ga duk wanda aka samu yana tauye ma’auni.
A zantawarsa da wakilinmu a cikin rangadin da ye je a kasuwar Bachaka da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar ya bayyana cewa ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da masu tauye ma’auni ba saboda wannan aikin ba ya tsaya a matakin masarautar Kabi ba a’a wannan aikin wani nau’i ne na jihadi saboda tauye yana haddasa musibu daban-daban tun kama daga rashin samun ruwan sama (fari) saukar da annoba da fitintinu daban-daban a cikin al’umma.
Sarkin Baki ya nuna rashin jinda ɗinsa bisa ga yadda waɗansu masu sana’ar sayar da abinci ke saka son rai a wajen gudanar da sana’o’in su ta hanyar tauye ma’auni ko haɗa mai kyau da mara kyau domin samun ƙazamar riba.
Ya ce ba za su lamuncewa duk wanda ya cigaba da aikata irin wannan ba kuma sun saka wani kwamiti na masu saka ido kan tauye ma’auni tare da ba su damar hukumta shi a dadin kasuwannin da ke akwai wannan yankin.
Mai Arewan Bachaka Alhaji Yakubu Maiyaƙi ya yaba wa Sarkin Bakin Kabi bisa kulawar da ya ke yi ga mutanen da ke sana’ar sakai faɗin masarautar Kabin Argungu.
Ya kuma yi alqawarin bayar da gudummawa wajen tabbatar an kawo gyara a cikin wannan aikin.
Wani dattijo da ya share sama da shekaru sittin yana gudanar da wannan sana’ar Alhaji Daudu Babbar Riga ya nuna damuwarsa dangane da jami’an tsaro da ke aiki kan wannan hanyar inda ya ce akwai a kalla shingen jami’an tsaro Arba’in da bakwai daga garin Bachaka zuwa Argungu da suka hada na hana fasakwabri, jami’an shige da fice, yansanda da jami’an tsaro na farin kaya da sauransu.
Shi kuwa Musa mainasara Bachaka ya dora laifin algussu bisa ga abokan kasuwancin su da ke Jamhuriyar Nijar saboda su ne ke tsallakowa nan Nijeriya su sayi buhunan abinci su koma da su Nijar su saka abincin a cikin ƙananan buhuna sannan su sake dawowa da shi suna sayarwa kuma a matsayin buhu amma yanzu in Sha Allahu za su ɗauki matakin gyara hulɗar kasuwanci da su don samun ɗorewar hulɗarmu da su.
