Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A matsayin wani ƙwaƙƙwaran mataki na tabbatar da gaskiya da tsaftace hukumar daga ɓatagari, Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin hanci da Rashawa, Ola Olukoyede, ya umurci ma’aikatan hukumar da su gaggauta bayyana kadarorinsu daidai da tanadin doka da ƙa’idojin aikin gwamnati.
Ya bayar da umarnin ne a ranar Talata a hedikwatar hukumar da ke Abuja yayin da ya ke jawabi ga manyan ma’aikatan EFCC.
Olukoyede ya jaddada cewa yaki da cin hanci da rashawa ya buƙaci waɗanda ke cikin harkar su tsaya kai da fata don cimma nasara.
“Dukkanmu za mu bayyana kadarorin mu; daga matakin aiki na 17, zuwa ƙasa. Na yi nawa, don haka babu wani dalili da zai sa kowa ya ji tsoron yin haka.
“Ko da Sakataren Hukumar ya yi, watakila ku ma kun yi a baya, amma akwai buƙatar mu sake yin hakan, za mu bayyana kadarorin mu, kuma za mu yi bincike a kai.
“Dole ne mu kafa misali mai kyau. A matsayinmu na masu yaƙi da cin hanci da rashawa, dole ne hannayenmu su kasance da tsafta, don haka dole ne mu bayyana kadarorinmu,” inji shi.
