Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani da ake zargin ɗan fashi da makami ne kuma carawon mota ya tsere daga gidan gyaran hali da ke Katsina.
Ana tuhumar ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Abba Kala da kitsa ayyukan fashi da sace-sacen motoci a Katsina, Filato da sauran jihohin da ke makwabtaka da su.
An ce, Kala ya yi amfani da wayarsa ne a lokacin da ake tsare da shi a gidan gyaran hali da ke Katsina wajen shirya wani manaƙisu da aka yi na kwace mota.
Kwamandan hukumar gidan yarin ta Katsina Muhammad Abdulmumini Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, tserewa daga hannun jami’an tsaro ba wani sabon abu ba ne.
“Ba sabon abu ba ne ga waɗanda ake zargi su tsere daga hannun jami’an tsaro. Mun ga haka tare da ‘yan sanda da ma sojoji da za su iya harbi a wurin.
“Gaskiya ne mutane biyu, waɗanda subke jira shari’a, sun tsere daga cibiyar gyaran halin. Na sanar da jami’an tsaron mu har ma na raba bayanan da wuraren ajiye motoci, idan an yi sa’a, za mu sake kama ɗaya yayin da muke zawarcin ɗaya,” inji shi.
Da yawa mazauna Katsina sun yi mamakin yadda mutanen biyu suka tsere daga wani wuri mai tsaro kamar gidan yari.
Sai dai hukumomin gidan yarin sun tabbatar da cewa babu wani abin fargaba saboda jami’an tsaro na kan bin sawun wanda ake zargin.
