Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Babban hafsan sojin Nijeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede (COAS), ya bada umarni mai ƙarfi ga dakarun haɗin gwiwa, Operations Fansan Yamma a Arewa maso Yamma, da su kara zage damtse, da nufin kawo ƙarshen fitaccen jagoran ‘yan bindigar nan Bello Turji, a raye ko gawar shi nan da kwanaki 30 masu zuwa.
Laftanar Janar Oluyede ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake jawabi ga dakarun Operation Fansan Yamma a hedikwatar runduna ta ɗaya dake Gusau a lokacin da ya ziyarci Jihar Zamfara yau Alhamis.
A cewarsa, umarnin ya zama dole idan aka yi la’akari da yadda Ƙasurgumin ɗan ta’addan Bello Turji ke ta’azzara hare haren rashin imani a jihohin Zamfara da Sakkwato da kuma wasu sassan jihar Kebbi domin ganin an samu zaman lafiya a yankin.
“Bana son jin labarin hare-haren Bello Turji da yake kai wa, musamman a jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi inda yake yawaita kai hare-haren ta’addanci a kan alumma, kuma na baku nan da kwana 30 ku yaƙi BelloTurji da muƙarraban sa a duk inda suke.
Hakazalika Laftanar Janar Oluyede ya shaida wa sojojin cewa na Najeriya dake ƙarƙashin sa cewar zai bada fifikon gaske wajen tabbatar da jin daɗin sojojin Ƙasar baki ɗaya .
Ya bayyana cewar, tuni aka ɓullo da wani tsari na musamman na mallakar gidaje don baiwa sojoji damar mallaka kafin su yi ritaya a farashi mai rahusa a faɗin ƙasar nan.
Ya kuma ƙara da cewa, za’a samar da isassun kayan aiki da tallafi ga sojojin domin basu damar yaƙar ‘yan ta’adda da sauran ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.
A cewar shi, ziyarar tashi nada nufin yaba wa ƙoƙarin da sojojin ke yi wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar da sauran jihohin Arewa maso Yamma da kuma ƙara musu karfi wajen yaƙi da ‘yan bindiga a yankin.
