Daga UMAar AKILU MAJERI Dutse
Ofishin asusun kula da rayuwar Ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da haɗa kai da gwamnatin Jihar Jigawa a ɓangarori da dama da suka haɗa da kiwon lafiya, ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare lafiyar Ƙananan yara, da al’umma baki ɗaya.
Shugaban ofishin na shiyyar kano, Mista Rahama Rihood Farah ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa a lokacin da yake karanta jawabinsa a ofishin gwamnan Jihar Malam Umar Namadi wadda ya Sami wakilcin mataimakin sa Injiniya Aminu Usman Gumel a ranar larabar da ta gabata.
Ya cigaba da cewa, haɗin gwiwar da UNICEF ta yi da gwamnatin Jihar Jigawa ya samu nasarori da daman gaske , kamar ƙarfafa tsarin tantance yaran da suke cikin kangin talauci, ta hanyar binciken da aka gudanar a kwanan baya (GHS), da samar da muhimman tsare-tsare da tsare-tsare, da kuma sanya masu ruwa da tsaki a tsarin.
Ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomin jihar da su bayar da gudunmawarsu wajen ganin shirin ya kai ga samun basara, domin magance halin ƙuncin rayuwa da ƙananan yara ke ciki a Jihar Jigawa, ta hanyar amfani da ƙwararan hujjojin da za a yi amfani da su domin tsara ɓangarori daban-daban.
Ya ce binciken ya nuna cewa kashi 90 bisa 100 na yara a Jihar Jigawa suna fama da matsanancin ƙangin talauci, yayin da kimanin kashi 86 bisa 100 ke fuskantar rashi a fannoni masu muhimmanci da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da abinci mai gina jiki, da tsaftataccen ruwan sha, da sauransu.
Mista Farah ya bayyana buƙatar haɗa hannu cikin gaggawa domin rage raɗaɗin talauci da inganta rayuwar yara a Jihar Jigawa.
“Don ƙarfafa ƙoƙarin mu na haɗin gwiwa, muna neman goyon bayan gwamnati wajen samar da matakan da za su tabbatar da yin amfani da bayanan da aka samu na ƙananan hukumomi domin gudanar da abin da ya dace”.
“Sauran fannonin sun haɗa da amincewa da ƙayyadaddun manufofin kare lafiyar jama’a, da amincewa da daftarin dokar kare al’umma da aka yi wa kwaskwarima zuwa doka, da ƙara yawan kason kasafin kuɗi don shirye-shirye na musamman na yara, da tabbatar da yin rajistar haihuwa ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar a duniya “, in ji Farah.
