Daga AISHA ASAS
Fitacciyar jarumar Hollywood, Zendaya, ta bayyana cewa, tana cikin shirin fitowa a sabon fim mai taken “A House Without Rain”, wanda zai taɓo batutuwan rashin tausayi da fuskantar rayuwa bayan rashi.
A cikin hirar da ta yi da mujallar Variety a ranar 30 ga Mayu, Zendaya ta ce, fim cin zai nuna yadda mace ke iya gina ƙarfinta daga karyewar zuciya da koma baya. Ta ce: “Ba kawai ina so in nishaɗantar da mutane ba, ina so in motsa tunani.”
Fim ɗin yana cikin shirye-shiryen da za a fara ɗauka a watannin Yuli zuwa Oktoba, tare da manyan daraktoci kamar Ava DuVernay da Anthony Hemingway. Masana Hollywood sun bayyana fim ɗin a matsayin wanda zai iya shiga gasar Oscar na shekarar 2026.
