Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tun asali dai Babban Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC), mallakin gwamnati ne, kuma har yanzu kamfani ne na gwamnati ne, wamda aka canja salon sa a watan Yuli, 2022.
Kamfanin yana alfahari da ɗimbin ababen more rayuwa da saka hannun jari a cikin ƙasa.
Kamfanin NNPC bisa doka yana tafiyar da harkokin haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da wasu kamfanoni na ƙasashen waje da suka haɗa da Royal Dutch Shell, Agip, EɗɗonMobil, TotalEnergies, Cheɓron, da Teɗaco (yanzu an hade su da Cheɓron). Ta hanyar haɗin gwiwa da waɗannan kamfanoni, gwamnatin Nijeriya na gudanar da aikin haƙo mai.
Bayan zartar da dokar masana’antar man fetur a watan Agustan 2021, kamfanin NNPC a yanzu yana gudanar da harkokin kasuwanci ba tare da dogaro da kuɗaɗen gwamnati kai tsaye ba.
A ranar 2 ga Afrilu, 2025, shugaban aasa Bola Ahmed Tinubu ya rusa kwamitin gudanarwar kamfanin na NNPC, ya naɗa Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin (GCEO). An naɗa Ahmadu Musa Kida a matsayin sabon shugaban da ba na zartarwa ba, wanda ya maye gurbin Cif Pius Akinyelure.
Ga cikakken jerin shugannin kamfanin NNPC daga 1977 zuwa yau:
1977-1980: Remilekun A Marinho
1980-1981: Odoliyi Lolomari
1981-1985: Lawrence Amu
1985-1990: Aret Adams
1990-1992: Thomas John
1992-1993: Edmund Daukoru
1993-1995: Chamberlin Oyibo
1995-1999: Dalhatu Bayero
1999-2003: Jackson G Obaseki
2003-2007: Funsho Kupolokun
2007-2009: Abubakar Yar’Adua
2009-2010: Muhammad Bakindo
2010: Shehu Ladan
2010-2012: Augustine O. Oniwon
2012-2014: Andrew Yakubu
2014-2015: Joseph Thlama Dawha
2015-2016: Ibe Kachukwu
2016-2019: Maikanti Baru
2019-2025: Mele Kyari
2025-yanzu: Bayo Bashir Ojulari
Wane ne sabon shugaban NNPC, Bashir Bayo Ojulari?
A ranar Larabar da ta gabata, 2 ga Afrilu, 2025, ne Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC).
Hakan ya biyo bayan yi wa kwamitin gudanarwar kamfanin garambawul tare da sallamar Mele Kyari da shugaban hukumar amintattu na kamfanin, Pius Akinyelure.
Bashir Ojulari ɗan asalin Jihar Kwara ne kuma ƙwawararren injiniya ne na Nijeriya wanda ya ƙware a fannin sinadaran man fetur, sarrafawa da kuma aikin injiniyanci.
Ya kammala karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria bayan ya karanta Mechanical Engineering tsakanin 1985 zuwa 1989.
Ojulari ya yi aiki a Elf a matsayin sabon wanda ya kammala digiri daga Satumba 1989 zuwa Oktoba 1991.
Ya koma Shell a watan Nuwamba 1991 a matsayin Associate Production Technologist a Shell Petroleum Deɓelopment Company (SPDC), bayan ya bar Elf Petroleum Nigeria a matsayin Injiniyan Filaye da Tsari.
Ya yi aiki a Shell sama da shekaru 24, inda ya zama Manajan Darakta na Shell Nigeria Eɗploration and Production Company (SNEPCo) a watan Nuwamba 2015, muƙamin da ya riƙe har zuwa Yuli 2021.
Sauran abubuwan da ya kamata ku sani game da Ojulari su ne:
Bayan ya shiga Shell a 1991, ya tashi ya zama memba na ƙungiyar Nazarin Haɗin kai a hedkwatar Shell a Netherlands a cikin Yuni 1994, matsayin da ya riƙe har zuwa Oktoba 1995.
Tsakanin Afrilu 1997 zuwa Nuwamba 1999, ya kasance Shugaban Tsare-tsaren Tattalin Arziki da Kasafin Kuɗi a SPDC na Nijeriya, inda ya tashi ya zama Jagoran ƙaddara kuma Shugaban Samar da Fasaha a Shell a Oman daga Disamba 1999 zuwa Satumba 2003.
Ya zama babban mai tsara yankin kudu da hamadar Sahara a hedkwatar Shell a watan Oktoba 2003 kuma ya rike mukamin har zuwa Disamba 2004.
Daga watan Janairun 2005 zuwa Oktoba 2008, ya kasance Manaja, Tsare-tsare da Dabarun kamfanoni a SPDC a lokacin kuma ya riƙe muƙamin Masanin Fasahar Samar da Kadarori a takaice daga Nuwamba 2006 zuwa Maris 2007.
A Shell, ya ci gaba da zama a Nijeriya tun daga nan, ya zama Manaja, Ci gaban Kadarori (Onshore and Shallow Water) SPDC daga Oktoba 2008 zuwa Oktoba 2010.
Daga watan Janairun 2010 zuwa Oktoba 2015, ya kasance Darakta na raya kasa a SPDC Nigeria, daga nan ya zama Manajan Darakta na SNEPco daga Nuwamba 2015 zuwa Yuli 2021 lokacin da ya bar kamfanin.
An naɗa shi mataimakin shugaban ƙasa kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin Renaissance Africa Energy Company a watan Janairun 2024, muƙamin da ya rikƙehar zuwa sabon naɗin nasa a matsayin shugaban NNPC.
Ya shiga harkar mai ne a daidai lokacin da kamfanin ke kammala sayen kadarar Shell a NIjeriya.
