Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Kawo yanzu dai a Nijeriya babu wanda bai san da labarin Kisan Gillar Uromi ba, wato ina nufin garin nan da ke yankin arewa maso gabashin ƙaramar Hukumar Esan a Jihar Edo, inda wasu ɓatagarin ’yan banga suka yi wa wasu mafarauta ’yan asalin Jihar Kano, su 16 kisan gilla tare da jikkata wasu da dama. Kodayake wasu rahotanni na bayyana cewa adadin waɗanda suka rasa rayukansu a wannan ibtila’i sun kai 19. Wannan babban abin takaici ya faru ne a yayin da mafarautan waɗanda ke cikin motar ɗaukar kaya ta kamfanin ɗangote, ke kan hanyarsu ta komawa gida Jihar Kano, don gudanar da bikin Sallah ƙarama tare da iyalinsu, bayan shafe tsawon lokaci a Kudu. Akan hanyar su suka ratsa ta garin Uromi da ke Jihar Edo inda suka gamu da wasu ’yan banga, waɗanda suka zarge su da kasancewa masu garkuwa da mutane, sakamakon ganinsu da bindigogin mafarauta.
Bidiyon yadda aka riƙa yi wa waɗannan bayin Allah da azal ta biyo da su wannan ƙauye, kisan gilla, ƙona su da ransu, da saran jikinsu da wuƙaƙe, ya karaɗe zaurukan sada zumunta, ya tayar da hankalin al’ummar ƙasa, musamman ma ’yan Arewa. Yayin da shugabanni da gwamnonin Arewa suka riƙa kiraye-kirayen a kwantar da hankali, kada a tayar da wata tarzoma, ko a far wa waɗanda ba su ji ba basu gani ba, da sunan ɗaukar fansa. Sannan aka tayar da jami’an tsaro suka bazama, domin sintiri a manyan biranen Arewa, cikin shirin ko-ta-kwana, da nufin daƙile duk wani abu da ka iya tasowa na fitina. Duk kuwa da kasancewar ana cikin lokaci ne na azumi.
Babu shakka ganin wannan bidiyo ya ɗaga hankalin mutane da dama, ba ma ni kaɗai ba, saboda irin mugunta da ƙetar da ɗan adam yake nuna wa ɗan adam ɗan uwansa, sakamakon zargin abin da ba a tabbatar ba, ɗanyen kai da rashin hankali, da kuma nuna ɓangaranci, ganin cewa mutanen Musulmi ne ’yan Arewa. Wannan rashin hankali da ƙiyayyar da ’yan Kudu ke nuna wa ’yan Arewa ba yau aka fara ba. A duk lokacin da aka ce an samu wata rashin fahimta ko yamutsi, sai tsageran su riƙa far wa duk wani ɗan Arewa ko dukiyarsa, da yi masa kisan wulaƙanci. Daga ɓangaren gabashi zuwa yammaci da kudancin ƙasar nan, ran ɗan Arewa da dukiyarsa ba a bakin komai suke ba. Ban da rayuwar ƙasƙanci da wulaƙanci da suke ciki, harwayau a kowanne lokaci wani abu ya tashi, wanda ya shafi siyasa ko addini, sai a nemi hucewa a kansu. Ana zargin su da ta’addanci ko wasu laifuka da wasu tsiraru ke aikatawa.
Kisan gilla wa matafiya da hanya ta ratsa da su wani yanki da ba nasu ba, na neman zama ruwan dare a ƙasar nan. Ba wannan ne na farko ba, da ake tare matafiya da tsautsayi ya bi da su ta wani yanki da ke fuskantar ƙalubalen tsaro, a yi musu kisan gilla, ko a cutar da su ba. A ranar 21 ga watan Agusta na shekarar 2021 wasu matasa daga ƙabilun Jihar Filato sun kashe wasu Musulmi su 26 da jikkata wasu da dama, yayin da suka ratsa ta yankin Kabong a ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, yayin da suka taso daga wajen taron Sabuwar Shekarar Musulunci daga Jihar Bauchi zuwa garin Ikare na Jihar Ondo.
Kamar yadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku da wasu malamai da shugabannin al’umma, suka yi ta kiraye-kirayen, lallai a nemo ɓatagarin da suka aikata wannan kisan gilla, don a hukunta su, kuma a biya diyyar rayukan da aka kashe, mun ji Babban Sufeton ’yan sanda na ƙasa yana ba da tabbacin an kama wasu da ake zargi da hannu a wannan aika-aika, har ma kuma Gwamnan Jihar Edo Monday Okpebholo, ya sanar da dakatar da duk wata ƙungiyar ’yan banga da ba gwamnati ce ta kafa ba. Sannan harwayau a yayin da nake wannan rubutu Gwamnan Jihar Edo da tawagar wasu manyan jami’an gwamnatin jihar sun ziyarci Jihar Kano, domin jaje da ta’aziyyar abin da ya faru, tare da bai wa al’ummar Kano haƙuri.
Ba wannan ne abin dubawa ba, amma me yake kawo irin wannan ƙeta da mugunta da ’yan Nijeriya ke nuna wa junansu, a dalilin wani saɓani ko bambancin addini ko aƙida. Abu ne mai bantakaici da banhaushi, a ce an mayar da ran ɗan adam kamar na kiyashi, ba a jin nauyin zubar da jini ko haddasa ɓarna. Daga jami’an tsaro har talakawa kowa ya samu damar riƙe makami sai ya nemi ran ɗan uwansa bisa wani kuskure ko zargin da bai taka kara ya karya ba.
A daidai lokacin da ’yan Nijeriya ke alhinin kisan gillar da aka yi wa mafarauta a Jihar Edo, a Babban Birnin Tarayya Abuja ma alhini ake yi sakamakon kisan gillar da jami’an tsaro suka yi wa wasu ’yan Shi’a da suka fita muzaharar nuna Allah wadai da kisan kiyashin da ƙasar Isra’ila take yi wa raunanan al’ummar Falasɗinu, kamar yadda suka saba yi duk shekara a kowacce Juma’ar ƙarshen azumi. A wata takardar sanarwa da ƙungiyar ‘Yan’uwa Musulmi a Nijeriya (IMN) ta fitar, mai ɗauke da sa hannun Farfesa Abdullahi ɗanladi, an zargi jami’an tsaro na Guard Brigade da kisan ’yan ƙungiyar mutum huɗu da kama masu zanga-zangar lumana su 380. Zargin da ƙungiyar kare haƙƙoƙin ɗan adam ta Amnesty International ita ma ta ƙara tabbatarwa, tare da yin Allah wadai da tauye haƙƙoƙin tsirarun mabiya aƙidar Shi’a da jami’an tsaro a Nijeriya ke yi.
Abin mamaki ne ganin yadda kururuwar kisan gillar Uromi ya ɗauke hankalin ’yan Nijeriya daga abin da ya faru a Abuja, duk da kasancewar shi ma ba sabon abu ba ne, jami’an tsaro su far wa masu zanga-zangar lumana a ƙasar nan. Amma yadda wasu ke kallon abin da ake yi wa ’yan Shi’a na kisa da kame a matsayin abin da ya dace, kuma an yi daidai, yana ƙara nuna yadda al’ummar mu ke rayuwa a makance, ba tare da iya rarrabewa tsakanin adalci da zalunci ba. Tsakanin daidai da rashin daidai. Yakamata a ko’ina ran ɗan adam ya zama abin girmamawa, kuma abin darajantawa, ba abin da za a riƙa murna don an kashe wanda ba ma addini ɗaya ko ba ma aƙida ɗaya ba. Amma kuma muna baƙinciki idan namu aka kashe.
Ran mafarauta da ran ’yan Shi’a duk rayuka ne, da ya kamata mu yi Allah wadai da duk wanda ya kashe su. Kuma mu nemi haƙƙin su bisa matakin doka, domin hana cigaba da irin wannan ɓarna. Dakta Aliyu Tilde, wani masanin ilimi ne da zamantakewa da ke Jihar Bauchi, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “RAI RAI NE: An yi kisan kai a garinmu a shekarar 1964, sai da Sarkin Bauchi na lokacin ya je, don girman laifin. Yau kuwa kowa kashewa ake yi, ko kashewa yake, ko shugaban ƙaramar Hukuma bai damu ba. Kisan mafarauta a Uromi da kisan Shi’a a Abuja duk kisa ne.”
Yayin da wani rahoto ke cewa, wai ’yan Shi’a ne suka fara harbin jami’an tsaro, shi ya sa suka mayar da martani mai tsauri, har zuwa rubuta wannan maƙala ba a fitar da gawar jami’in tsaron da aka ce sun kashe ba, ko sunansa. Kamar yadda muka ga wanda ’yan Shi’a suka fitar. Ba za mu taɓa goyon bayan ɓarna da tauye haƙƙi daga kowanne ɓangare na al’umma ba. Da jami’an tsaro, da mafarauta da ’yan Shi’a duk ’yan Nijeriya ne, kuma suna da haƙƙi a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasa.
Yakamata ’yan Arewa mu san inda yake mana ciwo, mu daina bari ana raba kawunanmu da bambance-bambance, na addini ko aƙida, don cin moriyar wasu. Yayin da ýan kudu ke yi mana kisan kiyashi ba tare da sun ware wannan daga wanne ɓangaren yake ba. A wajen su dukkan mu Hausawa ne, dukkan mu musulmi ne, dukkan mu Boko Haram ne, kuma dukkan mu masu garkuwa da mutane ne!
