Akwai wani batu da ke faruwa a duniya, wanda kusan kowa abin ya shafa, shine batun yaƙi dake wakana a gabas ta tsakiya. Wannan yaƙin, yaƙi ne da za a iya cewa, tsakanin Isra’ila ne, da kuma Hamas. Amman idan kayi tunani sossai, tare da zurfafa bincike zaka fahimci cewa, wani yunƙuri ne, na yakin duniya.
Kafin mu gano, zamu iya cewa, su wanene Hamas sannan su wanene Isra’ila. Yadda wasu ke tunani sam ba haka bane. Misali, Isra’ila, ba yadda wasu yan uwan mu kristawa ke tunani ba. Na’am akwai wani batu da yazo a littafin Bible, sura 15 aya ta 18, akan kasa ta alkawari. “Allah ya yayi wa Annabi Ibrahim alkawarin kasa, wannan ƙasar ita ce ake yaki akai yanzu, Isra’ila ta Falasɗinu. Ba iya nan, wasu a wurare da yawa, misali a littafin ƙur’ani, lokacin da Allah ya gaya Annabi Musa (As) dashi da iyalan jama’ar sa da su kaura zuwa Falasɗinu. Allah ya nuna musu ce wa kasa ce mai ni’ima tare da zaman lafiya. Mutanen da ke ciki waton Falasɗinawa zasu tarbe su hannu biyu biyu. Abinka da yahudawa, kamar yadda suka saba wahalar da Annabi Musa (As) wannan karon ma haka suka ce masa, “ya kai Musa, ka faɗawa Ubangijin ka ba zamu iya shiga wurin ba.
Hakazalika Hamas, ’yan asalin Falasɗinu, waɗanda suka taso a gwagwarmayar kare kasa, tare da yakin neman yanci daga waɗanda suke cutar da su. ƙasar Falasɗinu suma dadden wuri ne a tarihi, wanda kasa ce, da ke daman, ta su ce tun can asali. Basu zo daga wani waje ba, kuma basu kori kowa ba.
Saboda banbanci ra’ayi, wasu ƙasashe na ayyana Hamas a matsayin ’yan ta’adda, yayin da wasu na musu kallo a matsayin jarumai masu sadaukarwa.
Yanzu duniya ta rabu kashi atakaice, misali, tun bayan yakin duniya na 2, Hitla ya kashe Yahudawa da yawan su ya wuce tunani, Majalisar ɗinkin Duniya ta nemi a bawa Isra’ila yanci tare da samar musu da kasa na kan su. Wanda da za ka duba da kyau, za ka ga cewa ƙasar sam bata ma kai wani jiha a Nijeriya ba, amman saboda wata maslaha, sai aka nemi da a basu.
To tun daga wancan lokacin, yaƙi ya fara samun asali a yankin, yadda yau kusan shekara 70 da wani abu ana zubar da jini babu kakkautawa. Ganin haka yasa wasu daga cikin matasa suka yunkuri suka samar da wata ƙungiyar kare dangi mai suna Hamas.
Har’ila yau, muna magana ne yadda Hamas ta samo asali. Hamas kalma ce larabci, ma’ana hamasa ko masu hamasa a hausance. ƙungiyar cike take kamar siyasa, domin na da ban garori daban-daban, kamar fannin siyasa, da kuma fannin yaƙi, duka fannin kasuwanci. ƙungiyar ta yi ƙarfi sossai, wanda kusan ko yaushe damuwan su shi ne tsare gida tare da kare mutuncin Falasɗinu.
Babban abin dubawa a yaƙin da ke faruwa a yankin gabas ta tsakiya, shi ne, wannan yakin ba yaƙi ne na addini ba, a wanni fannin za a iya cewa yaki ne na ƙabilanci, amman sam ba haka bane. Idan aka ce yaki ne na addini kamar yadda wasu Kiristawa ke tunani a Nijeriya, sai ka duba da kyau, Isra’ila ba addinin Kirista suke bi ba, kuma akwai wasu masu bin addinin Kirista a cikin ƙungiyar Hamas.
Idan kuma mu ka yi duba i zuwa ƙabilanci, na’am zamu iya cewa haka, amman ko a cikin kwayar ƙasar Isra’ilan akwai Larabawa.
Hamas da Isra’ila, yaƙin nan yaƙi ne na manufa, sanda Isra’ila na anfani wajen yaƙar Falasɗinu domin ta daɗaɗa yankin na ta. Ma’ana, burin Isara’ila shine kawar da Falasɗinawa gaba dayan ta, sannan kuma ta kara samun ƙarfi, domin so take ta zama mamakin gabas ta tsakiya.
Su kuma sauran ƙasashen larabawa ina makomar su take? Maganar gaskiya, a wata manuniya da hasashen da ƙasar Isra’ilan take yi, akwai batun, bayan gamawa da Falasɗinawa , zata aukawa Siriya, da Jodan da kuma Lebanon. Kasar Iraki ma bata tsira ba. Hakan ya tabbata ne a wani map da wani jami’in gwamantin ƙasar ya fitar ya nuna duniya.
Wannan shine ajandar su ta farko, kana daga bisani, za a hallaka Iran, da sanan Saudiyya da wasu ƙasashen daular Larabawa ma ba za su tsira ba.
To amman tayaya za a gama da Falasɗinawa? Ana gizon ke sakar. Ba a iya gamawa da Falasɗinawa ba saboda ’yan gwagwarmayar Hamas, domin sune garkuwan ƙasar ta Falasɗinu. ƙasashen yamma irin Amurka da U.K da da Faransa, kawaye ne Isra’ila, sun daɗe sunana goyon baya tare da tallafawa Isra’ila, burin shine a kawar da Hamas sannan Falasɗinun ba gaba ɗaya ta tashi aiki. Idan baku manta ba, shugaban Amurka, Donal Trump, yayi wani yunkuri, a wani salo nashi na yaudara. Bayan hawan sa mulki wa’adi na biyu, nuna mutum ne mai son zaman lafiya, ta inda ya goyi bayan a tsaida wuta. A wannan yanayin ya kara neman Falasɗinawa da fice su shiga ƙasashen ketare, kamar su Misra da Jodan, sannan yayi yunƙurin sake gina gaza. Ya wallafa wannan a shafi sa na ɗ, inda ya nuna cewa zai maida Gaza Aljannar duniya.
Mai karatu ina fatan yanzu ka gane su wanene Hamas, kuma Mene ne aikin, to nenene bambancin su da Isara’ila, bayan kowa yana ɗauki da makamai. Na’am, dukan su mayaka ne, kowa na dashi manufa. Manufar Hamas kare Falasɗinu, su kuma Isra’ila faɗaɗa Isra’ila.
Amman wani babban bambanci shine, Isra’ila burin ta, kashe kowa da kowa ne a Falasdinu. Shi yasa sun kashe mata, yara, harda tsofofi. Yayin da su kuma Hamas, kare kai suke, iya sojoji suke kashe wa, shi yasa zaiyi wuya kaga wani yaro wanda Hamas ta kashe a isra’ila.
Mai karatu ya kamata ka gane, yanzu wannan yaƙin ya raba duniya gida biyu, inma kana Isra’ila, ko kana Falasɗinu. Idan mukayi duba, saka fahimci cewa, wa’yanda suke da Isra’ila sun haɗa ne da ƙasar Amurka, U.K, Faransa, da duk wani kasa da ke yamma. Yayin da, Rasha, China, Iran, Koriya da Arewa da Yamen, suna tare da Falasɗinawa.
To yaushe yakin nan zai zo karshe. Na’am, ko a fittafin Bible, an nuna cewa za ayi ya yakin, har sai Yesu ya bayyana. A bangare guda kuma, tarihi na nunawa, kusan haka ne, za a yi ta yakin har sai Mahadi (As) jikan Annabi da Annabi Isa (As) Yesu sun dawo.
Masu goyon bayan Isra’ila idon su ya rufe, a makance suna goyon bayan su, ba tare da sunyi la’akari da jinin da ake zubarwa ba. ƙalilan ne masu goyon bayan raunana da ake kashewa a Falasdinu, kusan a tunanin zan iya kiran su masu ƙarfin imani.
Ba iya kasashen Iran da China da Rasha ke goyon bayan Falasɗinu ba, hatta a cikin ƙasashen turawan, akwai mutane da suke ganin abinda akewa Falasɗinu ɗin yayi yawa, kamata ne a basu yancin su, su zauna lafiya, su shaƙi iska kamar yadda wasu ke shaka.
Yanzu inane makomar Falasɗinu, shin za su ƙare kuwa? Duk da ma wata sabuwar siysa ta fara aukuwa, yadda su kan su sun fara rabuwa, wasu na tunanin yaƙar Hamas. Amman duk da haka, Hamas sune garkuwan Falasɗinu, babu Hamas, to babu Falasɗinu.
Mai karatu, da fatan ka fahimci su wanene Hamas, sannan su wanene Isra’ila. Kamar yadda mukayi bayani manufofin su da kuma yadda yakin gabas ta tsakiya ta kunsa. Gaskiya mutane na mutuwa sossai, jini na zuba, ta yadda ba za a iya kwatanta wa ba. Idan kana da wani karin bayani, ko karin ilimi ko tambaya, ƙofa a buɗe take. Da fatan Allah zai taimaki bayan sa, tare da da kawo ƙarshen zubar da jini da ke aukuwa a yankin.
Wasiƙa daga MUHAMMAD ALBARNO. 08034400338.
