Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin kafa wuraren al’adu da tarihi a ƙarƙashin nan na nata na ‘Renewed Hope’, wato Sabuwar Nijeriya, a faɗin Nijeriya, domin kiyaye al’adun gargajiyar Najeriya, bunƙasa harkokin yawon buɗe-ido da uwa uba bunƙasar tattalin arziki.
Abiola Abdulkareem, mataimaki na musamman ga ministar fasaha, al’adu, da yawon buɗe ido, Hannatu Musawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, a Ilorin, Nihar Kwara.
A cewarsa, shirin ya samu amincewar Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa kuma za a aiwatar da shi tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa wuraren ƙirƙire-ƙirƙire da samar da ayyukan yi a fannin fasaha da nishaɗi.
“Nasarar aikin ta dogara ne kan yadda gwamnatocin jihohi, al’ummomin ƙananan hukumomi, da masu ruwa da tsaki da suka shiga cikin aiki. Ta hanyar yin aiki tare, Najeriya za ta iya ba da damar kawo sauyi a ɓangaren fasaha, al’adu, yawon shaƙatawa da masana’antu don samar da ci gaba mai ɗorewa da haɗin gwiwar zamantakewa,” inji Abdulkareem.
Ya yi bayanin cewa, shirin zai mayar da hankali ne wajen maido da adana wuraren tarihi, kayayakin tarihi, manyan fadoji, da kayayyakin tarihi tare da inganta ilimin al’adu da inganta sana’o’in gida.
Abdulkareem ya jaddada cewa, shirin ya yi daidai da ajandar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ‘Renewed Hope’ kuma ana sa ran zai samar da dubunnan ayyukan yi da kuma ƙara haɓaka kuɗaɗen shiga ta hanyar yawon buɗe ido da kuma masana’antu.
Ya jaddada aniyar Musawa ta bunƙasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar sabbin tsare-tsare da manufofi ta hanyar ƙulla kawance a masana’antar ƙere-ƙere.
Ya ƙara da cewa, “Wannan shiri ba kawai zai bunƙasa ɓangaren ƙere-ƙere na Najeriya ba, har ma zai taimaka matuƙa wajen haɓaka tattalin arziki da ci gaban ƙasa.”
