Rikicin hawan sallah: Rundunar ƴan sanda ta gayyaci Sarki Sanusi zuwa Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙoƙarinta na bincike game da musabbabin faruwar rikici da ya auku a yayin bukukuwan Sallah a Kano, rundunar ƴan sanda ta gayyaci Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II zuwa Abuja.

A ranar 30 ga watan Maris ne aka samu rikicin da ya haɗa da fadawan Sarkin, wanda ya yi sanadin mutuwar ɗan bijilante ɗaya da raunata wasu.

Daga bisani, ƴan sanda a Kano sun kama wani matashi mai suna Usman Sagiru ɗan shekara 20 da hannu a rikicin.

Hukumomi sun gudanar da bincike akan Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, inda suka masa wasu tambayoyi.

A takardar gayyatar da ke ɗauke da sanya hannun Kwamishinan ƴan sanda ɓangaren ayyuka, CP Olajide Rufus Ibitoye, Sanusi zai halarci reshen Leƙen Asiri na Hedikwatar ƴan sandan, a ranar Talata, 8 ga watan Afrilu, 2025 da misalin ƙarfe 10 na safe.

An rubuta takardar ne a ƙarƙarshin umarnin Sufeto Janar na rundunar.

Gabannin Sallah ne suka fitar da sanarwar hana bukukuwan salla da aka saba yi a duk shekara sakamakon barazanar tsaro a Jihar Kano.

Duk da haka, sai da Sarki Sanusi ya gudanar da hawan sallar, wanda ya na ɗaya daga cikin ababen da hukumomin tsaron suka hana.

By Babaji