BIDIYO: Shettima ya dawo daga Senegal bayan ziyarar kwana ɗaya

Spread the love

Mataimakin Shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ya dawo Abuja bayan ziyarar kwana ɗaya da ya kai ƙasar Senegal, inda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kan ƙasar.

A lokacin ziyarar tasa, Sanata Kashim Shatima ya halarci bukukuwan murnar samun ‘yancin kai na al’ada da aka gudanar, ciki har da wani faretin ban-girma da aka yi akan titin Mamadou Dia dake babban birnin ƙasar, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bassirou Diomaye Faye.

Wakilan Najeriya a taron sun haɗar da
Ministan harkokin waje Ambassador Bianca Odumegwu Ojukwu da Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai Mai kula da Harkokin Waje, Hon Oluwole Oke.

By ukarofi