Jigawa 2027: Yadda haɗakar Badaru da Lamido ke barazana ga siyasar Namadi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A jihar Jigawa, inda siyasa ta daɗe tana tafiya a ƙarƙashin manyan jiga-jigai masu ƙarfi, tsarin shugabanci mai zurfi da kuma ƙawance na siyasa da aka gina tsawon lokaci, fafatawar neman kujerar gwamnati gabanin zaɓen shekarar 2027 na ƙara zama zaya daga cikin mafi zafi da tayar da ƙura a tarihin dimokuraɗiyyar jihar.

Abin da tun farko ya yi kama da tafiyar sake zaɓen Gwamna Umar Namadi cikin sauƙi, yanzu yana rikiɗewa zuwa wata babbar arangamar siyasa mai cike da sauyin aminci, rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar APC, dawowar jam’iyyar PDP da kuma haɗuwar wasu manyan masu ruwa da tsaki a siyasar Jigawa.

A tsakiyar wannan sabon yanayin siyasar akwai Gwamna Umar Namadi na APC da kuma Mustapha Sule Lamido na PDP, waɗanda gogayyarsu ke ƙara sauya fasalin siyasar Jigawa gabanin zaɓen 2027.

Duk da cewa Gwamna Namadi na ci gaba da cin moriyar kasancewa a kan mulki, wanda ya haɗa da iko da tsarin gwamnati, naɗe-naɗe da kuma ƙarfin mulki, rahotanni na nuna cewa Mustapha Sule Lamido na ci gaba da gina wata babbar haɗaka da masana siyasa ke ganin za ta iya girgiza mulkin gwamnan.

Rahoton ya nuna cewa fitowar Mustapha Sule Lamido a matsayin ɗan takarar gwamna na bai ɗaya na PDP ya ƙara nuna cewa jam’iyyar na son kauce wa rikicin cikin gida tare da mayar da hankali gaba ɗaya wajen ƙalubalantar APC.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Dakta Aminu Taura, ne ya gabatar da ƙudirin amincewa da Mustapha Sule Lamido a matsayin ɗan takarar bai ɗaya, yayin da Wada Abubakar Dokaji ya mara masa baya a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar tare da shugabannin PDP daga ƙananan hukumomi 27 na jihar.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban PDP na jihar, Babandi Ibrahim, inda aka amince da Lamido ta hanyar ƙuri’ar murya.

Mustapha Sule Lamido, wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ba sabon suna ba ne a siyasar jihar.

A zaɓen gwamnan Jigawa na shekarar 2023, shi ne ɗan takarar PDP inda ya bai wa APC ƙalubale mai ƙarfi. Duk da haka, Gwamna Umar Namadi ya yi nasara da ƙuri’u 618,449 bayan da ya lashe ƙananan hukumomi 26 cikin 27 na jihar.

Mustapha Sule Lamido ya samu ƙuri’u 368,726, yayin da Ibrahim Ringim na NNPP ya samu ƙuri’u 37,156.

Tun bayan zaɓen, Mustapha Sule Lamido ya ci gaba da gudanar da ayyukan siyasa a matakin ƙasa, yana ƙarfafa tsarin PDP tare da jawo matasa da masu goyon baya.

Masu goyon bayansa na ganin shi a matsayin sabon jigon siyasa mai ƙoƙarin kawo sauyi ta hanyar gyaran tsarin gwamnati, bunƙasa cibiyoyi da kuma ƙarfafa matasa.

Bayan amincewa da shi a matsayin ɗan takara, Lamido ya buƙaci mambobin PDP su haɗa kai domin ceto Jigawa daga matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da yake zargin jihar na fuskanta.

Ya ce fannonin lafiya da ilimi na cikin mawuyacin hali, yana mai cewa PDP dole ta yi duk mai yiwuwa wajen kare muradun jam’iyyar da kuma na jihar.

Sai dai babban sauyin da ke sauya yanayin siyasar Jigawa shi ne ƙara tsanantar rikici tsakanin Gwamna Umar Namadi da wanda ya gabace shi, tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.

Tsawon shekaru, ana kallon Badaru a matsayin jagoran siyasar da ya taka muhimmiyar rawa wajen fitowar Namadi a matsayin gwamna. Amma majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya fara ne watanni kaɗan bayan Namadi ya hau mulki sakamakon saɓani kan naɗe-naɗe da ikon siyasa.

Rahotanni sun ce babban ɓarakar farko ta bayyana ne yayin shirye-shiryen rantsar da sabuwar Majalisar Dokokin Jigawa a watan Yunin 2023.

A wani taron masu ruwa da tsaki da Badaru ya kira a Kano, an ce ya shawo kan Namadi ya goyi bayan sake zaɓen Idris Garba Jahun a matsayin Kakakin Majalisar domin ci gaba da tsarin rabon muƙamai.

Sai dai daga baya Namadi ya sauya matsayi tare da mara wa Aliyu Dangyatin daga mazaɓar Miga baya.

Rahotanni sun nuna cewa matakin ya fusata ɓangaren Badaru, musamman ganin yadda tsohon gwamnan ya halarci zauren majalisar domin tabbatar da zaɓen Dangyatin.

Tun daga lokacin ne masana siyasa suka fara ganin rikicin neman iko tsakanin Namadi da Badaru ya fara ɗaukar sabon salo.

Daga baya rikicin ya sake ƙara tsananta bayan Majalisar Dokokin Jigawa ta amince da rahoton Kwamitin Kula da Asusun Jama’a wanda ya ba da shawarar binciken zargin almundahana da aka danganta da gwamnatin Badaru tsakanin 2019 zuwa 2024.

Rahoton ya ambaci zarge-zargen saye-sayen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, kashe kuɗaɗe ba tare da bayani ba da kuma wasu bayanan kuɗi da suka ɓace.

Masu biyayya ga Badaru sun fassara matakin a matsayin siyasa ce ta ramuwar gayya, duk da cewa majalisar ta ce aikinta ne na sa ido.

A halin yanzu, rahotanni na nuna cewa ɓangaren Badaru da na Sule Lamido na ci gaba da tattaunawar haɗin gwiwa domin marawa Mustapha Sule Lamido baya a zaɓen gwamna mai zuwa.

Majiyoyi sun ce magoya bayan Badaru na iya tallafa wa PDP domin samun wasu muhimman muƙamai kamar mataimakin gwamna da kujerun majalisa.

Ko da yake Badaru ya musanta zargin cewa yana shirin ficewa daga APC, hulɗarsa da wasu jiga-jigan adawa na ci gaba da haifar da raɗe-raɗi.

Masana siyasa na ganin cewa haɗuwar Sule Lamido da Badaru Abubakar babbar barazana ce ga siyasar Gwamna Namadi.

Mashahurin mai sharhin siyasa, Abdullahi Ubale Gumel, ya bayyana cewa idan har waɗannan manyan jiga-jigai biyu suka haɗa kai gaba ɗaya wajen marawa Mustapha Sule Lamido baya, to Gwamna Namadi zai fuskanci gwagwarmayar siyasa mafi girma a rayuwarsa.

Ya ce, Sule Lamido na daga cikin fitattun jagororin siyasar Jigawa da suka mallaki gagarumin tasiri a matakin ƙasa, yayin da Badaru ya gina ƙaƙƙarfan tsarin siyasa a APC.

Sai dai Gumel ya ce har yanzu Namadi na da wasu manyan damar da za su iya taimaka masa, musamman kasancewa gwamna mai ci da kuma yiwuwar samun cikakken goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC ta ƙasa.

Ya kuma yi zargin cewa akwai wasu manyan jami’an gwamnati da naɗaɗɗun muƙamai da za su iya yin aiki a ɓoye domin taimaka wa sansanin Badaru da Mustapha Sule Lamido.

A cewarsa, babban haɗarin da ke gaban Namadi shi ne yiwuwar samun masu yi masa zagon ƙasa daga cikin gida fiye da barazanar ’yan adawa.

Yayin da siyasar Jigawa ke ƙara ɗaukar zafi, abin da ya fara a matsayin tafiyar sake zaɓen gwamna cikin sauƙi yanzu ya rikiɗe zuwa wata babbar arangamar siyasa mai cike da sauyin aminci, sabbin haɗaka da fafatawar neman iko.

By ukarofi