Jihar Zamfara ta yi zarra a Arewa a jarrabawar NECO 2024

Spread the love


Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja

Jihar Zamfara ta shiga jerin jihohin Arewa da su ka yi abun a zo a gani a jarrabawar NECO lokacin da hukumar ta fitar da sakamakon jarrabawa na rukunin ɗalibai masu hazaƙa.

Wannan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwaman jihar, Sulaiman Bala Idris, ya yi. Ya bayyana cewa a faɗin kasar, Jihar Zamfara ita ce ta zo na biyu da ɗalibai 35, yayin da Jihar Anambra ta zo na farko.

Ya bayyana cewa, a karo na farko Jihar Zamfara ta zo na biyu a wannan jarabawar wanda ɗalibai ne ƴan ƙasa da shekara 11 suke rubutawa.

Makarantar Gwamnatin Tarayya da ke Suleja, ita ce makarantar da ke horar da irin wannan ɗaliban. Ɗaliban suna samun damar tallafin Gwamnatin Tarayya.

Ya bayyana Jihar Zamfara za ta cigaba da yin abun a zo a gani a wannan fannin.

By ukarofi