Jonathan da Obi sun yi ganawar sirri a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan da ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, sun ja labule a Abuja domin tattauna muhimman al’amuran ƙasa, ranar Alhamis.

Peter Obi, wanda ya sanar da ganawar ta shafinsa na X, ya bayyana Jonathan a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasa kuma babban wa a gare shi.

Zuwa lokacin kammala haɗa rahoton, ba a samu cikakken bayani game da abinda tattaunawar ta ƙunsa ba, saidai masu sharhi na ganin hakan bai rasa nasaba da batun shugabanci, tattali da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fama da su a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Majiyoyi da ke kusa da jagororin sun bayyana cewa tattaunawar ta ginu ne akan al’amuran da suka shafi ƙasa da suka haɗa da gyare-gyaren tattali, dawo da martabar zaɓe da kiraye-kiraye akan shugabancin damawa da kowane ɓangare.

Jonathan, wanda ya shugabanci Nijeriya daga 2010 zuwa 2015, ya zama jigo wajen ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ci-gaban dimukraɗiyya a ƙasashen Afirka, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin jakadu na musamman akan shiga tsakani wajen magance rikici da sanya ido a zaɓuka.

Haka kuma, ana ganin ganawar ta zama tubali na yin haɗaka tsakanin jagororin a yayin tunkarar babban zaɓen 2027.

By Babaji