Kaduna: Dalibai a makarantar mata sun koka kan rashin ruwan sha da banɗakuna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dalibai mata na Makarantar Firamare ta Jalo Model da ke Rigachikun a Jihar Kaduna sun nuna damuwarsu kan ƙarancin kayayyakin tsafta da ruwan sha a makarantar, lamarin da suka ce yana shafar karatunsu.

Sun bayyana cewa rashin isassun bandakuna masu tsafta da kuma ruwan sha mai kyau na hana su maida hankali a aji tare da kiyaye tsaftar jikinsu, musamman a lokutan karatu.

Yawancin ɗaliban, waɗanda ke aji na Basic Nine, sun bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ƙungiyar Education as a ɓaccine (EɓA) ta kai makarantar domin ƙarfafa gwiwar ‘yan mata su riƙa bayyana matsalolin da ke shafar karatunsu a jihar.

ɗaya daga cikin ɗaliban, Khadija Muhammad, ta ce ilimi yana da matuƙar muhimmanci ga ‘ya’ya mata, kuma ya kamata a tallafa musu ta hanyar samar da kayayyakin tsafta da kayan koyo domin su samu damar yin fice.

“Ba mu da ruwa a makaranta, sannan bandakuna ba su da tsafta kuma ba su isa ba. Yawanci yara maza suna yin bayan gida a waje, wanda ke ƙazantar da muhalli.

Mu kuma muna zuwa gidajen makwabta domin yin bayan gida saboda muna buƙatar ruwa don wanke kanmu bayan mun gama,” in ji ta.

Amaturrahman Ahmad, wadda ke burin zama likita a nan gaba, ta ce tana farin ciki da iyayenta suka ba ta damar zuwa makaranta sabanin wasu ‘yan mata a unguwarsu da ba su samu wannan dama ba.

Ta ƙara da cewa rashin ruwa da bandakuna masu kyau na hana ta maida hankali sosai a karatu, tana mai kira ga gwamnatin jihar da ta samar da kayayyakin tsafta tare da ɗaukar ma’aikatan tsafta domin kula da su.

Wata ɗaliba kuma, Hauwa’u Yahya, ta bayyana wasu ƙalubalen da makarantar ke fuskanta, ciki har da rashin kujeru, ƙofofi da allo.

A cewarta, malamai na yin iya ƙoƙarinsu wajen koyarwa, amma yawan ɗalibai a aji na hana kowa fahimtar darasin yadda ya kamata.

“Muna kusan ɗalibai 150 a aji ɗaya. Ina kira ga gwamnati ta zo makarantar mu ta ga halin da muke ciki, ta taimaka mana da ƙarin ajujuwa, ƙofofi da tagogi.

Ba mu da ruwan sha, don haka muna roƙon a hako mana rijiyar burtsatse domin mu samu ruwa,” inji ta.

Da take jawabi tun da farko, wakiliyar EɓA, Mercy Abalaku, ta ce shirin mai taken “Fostering Accountability for Girls’ Education” yana haɗa ‘yan mata da masu yanke shawara da ƙungiyoyin sa ido domin su raba ƙwarewarsu tare da neman mafita.

Ta ce binciken da aka gudanar tsakanin shekarun 2020 zuwa 2023 ya nuna cewa har yanzu ana fuskantar ƙalubale kamar ƙarancin gine-gine, cin zarafin jinsi, matsalolin lafiyar haihuwa da kuma rashin wadatattun kayayyakin WASH a makarantu.

Abalaku ta ƙara da cewa duk da cewa ana ware kuɗi mai yawa ga fannin ilimi a jihar — fiye da ƙa’idar UNESCO — har yanzu akwai gibin kayayyaki a makarantu.

A nata ɓangaren, shugaban aji shida na makarantar, Zakari Isah, ya bayyana shirin a matsayin mai muhimmanci, yana mai cewa ‘yan mata na buƙatar shiriya da wakilci saboda ƙalubalen da suke fuskanta tun suna ƙanana.

Sai dai ya jaddada cewa makarantar na fama da matsalolin rashin wutar lantarki, ƙarancin ruwa da kuma rashin tsaftatattun bandakuna.

Ya ce duk da cewa rijiyar burtsatsen makarantar na aiki, ba a iya janyo ruwa saboda rashin janareta, yana mai ƙara da cewa satar kayan makaranta, ciki har da na ɗakin kwamfuta, na daga cikin matsalolin da suke fuskanta.

Isah ya yi kira ga gwamnati da ta fifita batun tsaro tare da magance matsalolin wutar lantarki da tsafta domin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantar.

By ukarofi