Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna
Shugaban ƙungiyar Capacity Movement ta ƙasa, Shehu Sani Sado, ya buƙaci tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna kuma tsohon ɗan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Rt. hon. Yusuf Ibrahim Zailani, da ya kwantar da hankali tare da bai wa zaman lafiya da haɗin kai fifiko dangane da rikicin da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a Jihar Kaduna.
Alhaji Shehu Sani Sado ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan dambarwar siyasar da ta kunno kai a ƙaramar Hukumar Igabi, inda ya jaddada muhimmancin kauce wa kalamai ko matakan da za su iya ƙara rura wutar rikici a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Haka kuma, ya buƙaci mai bai wa Gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkokin siyasa, Honarabul Abubakar Mamadi, da ya fito ya janye kalaman da ake dangantawa da shi kan batun rubuta sakamakon zaɓe, domin kare martabar tsarin dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da amincewar jama’a ga harkokin zaɓe.
A ƙarshe, shugaban na Capacity Moɓement ya yi kira ga jam’iyyar APC da ta tabbatar da adalci, gaskiya da riƙon amana ga dukkan ɓangarorin da lamarin ya shafa, yana mai cewa hakan ne kaɗai zai tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya da cigaban jam’iyyar a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
