Bayan shafe kwanaki 36 a hannun ‘yan bindiga, yaran makaranta da wasu sun kuɓuta a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Bayan shafe kwanaki 36 a hannun masu garkuwa da mutane, yara makaranta shida, direbansu da wasu manya biyu da aka sace a Jihar Kaduna sun samu ‘yancinsu tare da komawa gidajensu lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa waɗanda abin ya shafa sun samu ‘yanci ne a ranar Lahadi, kafin su isa gidajensu da safiyar Litinin bayan sun yi tafiyar kusan sa’o’i shida a cikin daji.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar Raya Al’ummar Kuturmi (KUDA), Malam Manasseh Samuel, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana jin daɗinsa kan dawowar mutanen gida bayan fiye da wata guda suna tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Ya gode wa dukkan waɗanda suka bayar da gudunmawa, addu’o’i da goyon baya domin tabbatar da samun ‘yancin waɗanda aka sace.

“Muna godiya ga duk wanda ya tsaya tare da mu a wannan mawuyacin lokaci. Komawarsu gida cikin ƙoshin lafiya babban abin farin ciki ne ga iyalansu da al’umma baki ɗaya,” in ji shi.

Yadda Aka Sace Su

An sace yaran makarantar, direban motarsu da wasu fasinjoji biyu ne a ranar 26 ga Afrilu, 2026, lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari kan wata mota da ke ɗauke da ɗalibai daga ƙauyen Akwando zuwa garin Kachia, hedikwatar ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Mutane tara ne aka yi garkuwa da su a harin, yayin da wata ƙaramar yarinya ta rasa ranta, lamarin da ya haifar da firgici da damuwa a tsakanin iyaye da mazauna yankin.

A cewar Samuel, bayan sakin su, waɗanda aka sace sun yi tafiyar kusan sa’o’i shida ta cikin daji kafin su isa gidajensu.

Wani jagoran al’umma kuma tsohon mai taimaka wa marigayi Gwamnan Kaduna, Sir Patrick Ibrahim Yakowa, kan harkokin yaɗa labarai, Mista Reuben Buhari, shi ma ya tabbatar da sakin mutanen.

Ya ce: “Bayan kwanaki 36 da aka yi garkuwa da su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makaranta daga Akwando zuwa Kachia, yara shida, direbansu da wasu manya biyu sun samu ‘yanci kuma sun dawo gida bayan tafiyar sa’o’i shida a cikin daji.”

Buhari ya bayyana cewa yaran sun fuskanci matsananciyar wahala a lokacin da suke hannun masu garkuwa da mutane, lamarin da ya sa suka rasa kusan zangon karatu guda ɗaya.

“Waɗannan yara sun fuskanci mummunar jarabawa kuma sun rasa kusan zangon karatu gaba ɗaya. Duk da haka, muna godiya ga Allah da suka dawo da ransu,” in ji shi.

Lamarin ya sake jawo hankalin masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da masu kare haƙƙin yara kan tasirin rashin tsaro ga ilimi da walwalar yara.

Duk da murnar dawowar waɗannan mutanen, Buhari ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da addu’a domin samun ‘yancin sauran mutanen da har yanzu ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane a yankunan Kudancin Kaduna.

Ya ambaci mutanen da aka sace daga ƙauyukan Awon da Ariko, waɗanda har yanzu suke tsare.

“Mu ci gaba da addu’a domin waɗanda aka sace daga Awon da suka kwashe kwanaki 42, da kuma na Ariko da suka kwashe kwanaki 57 a hannun masu garkuwa. Muna fatan watan Yuni zai zama watan ‘yanci ga dukkan waɗanda ke tsare,” in ji shi.

Sakin mutanen ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar hare-haren sace-sace da matsalar rashin tsaro a wasu sassan ƙaramar Hukumar Kachia da ma yankunan Kudancin Kaduna gaba ɗaya. Jama’a na ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma ceto sauran waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane.

By ukarofi