Asusun bunƙasa ababen more rayuwa na iskar gas ya zuba biliyan N430 a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Asusun Tallafa wa Bunƙasa Ababen More Rayuwa na Iskar Gas a Fannin Harkokin Mai (MDGIF) ya bayyana cewa, zuba jarin da asusun ya yi a ɓangaren iskar gas a Nijeriya ya haura Naira biliyan 430, lamarin da ya jawo jimillar jarin da ya kai kusan Naira tiriliyan 1.6 daga masu zuba jari masu zaman kansu.

Babban Daraktan Asusun na MDGIF, Oluwole Adama, ne ya bayyana hakan yayin bikin ƙaddamar da Babbar Tashar CNG mai ƙarfin aiki ta kamfanin Rolling Energy, wanda Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar.

A baya dai, Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta sanar a watan Nuwamban 2025 cewa asusun MDGIF ya ware sama da naira biliyan 287 domin bunƙasa ababen more rayuwar iskar gas a sassan ƙasar nan.

Da yake jawabi ta bakin Daraktan Gudanar da Ayyuka na MDGIF, Hussaini Basaka, Adama ya bayyana cewa asusun ya mallaki kaso 45 cikin 100 na aikin Rolling Energy.

Adama ya ce, zuwa yanzu asusun ya zuba jari a ayyukan samar da ababen more rayuwar gas guda 31, waɗanda suka haɗa da cibiyoyi 125 na gas a faɗin ƙasa.

A cewarsa, an riga an ƙaddamar da goma daga cikinsu, yayin da sauran ke matakai daban-daban na kammalawa.

“Mun gina babban tsarin ayyuka da ya haɗa da manyan tashoshi, ƙananan tashoshi, cibiyoyin LNG da hanyoyin sufuri da za su tallafa wa masana’antu da ɓangaren sufuri. Burinmu shi ne rage farashin makamashi, ƙarfafa amfani da makamashi mai tsafta da kuma jawo ƙarin jarin masu zaman kansu a fannin gas,” inji shi.

Shugaba Tinubu ya bayyana jerin ayyuka huɗu da asusun MDGIF ya tallafa musu kuma aka ƙaddamar a ranar Juma’a. Ayyukan sun haɗa da tashar FEMADEC Energy da ke cikin Jami’ar Tarayya ta Fasaha da ke Owerri (FUTO), wadda ita ce ta farko cikin tashoshin CNG guda 20 da za a gina a jami’o’in Gwamnatin Tarayya.

Sauran sun haɗa da cibiyar Portland Gas da ke Ojota a Legas, cibiyar Ibile Oil and Gas mai tashoshin CNG guda 15 a Legas, da cibiyar Rolling Energy da ke Jahi a Abuja, wadda ke jagorantar wasu cibiyoyi 17 na RLNG da LCNG a jihohin Kaduna, Kano da Borno.

Shugaban Shirin Bunƙasa Amfani da CNG na Fadar Shugaban ƙasa (PCNGI), Barista Ismaeel Ahmed, ya bayyana cewa, shirin ya jawo gagarumin zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu.

Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Sadarwar Zamani da Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai, O’Tega Ogra, ya ce, gwamnati ta samar da hanyoyin samun rance domin taimaka wa masu motoci su sauya zuwa amfani da CNG.

A wani ɓangare kuma, bayanan PCNGI sun nuna cewa, Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin bada rancen naira biliyan 2.5 tun a watan Maris na 2025, domin ƙarfafa sauya motoci zuwa CNG da kuma samar da kayan aikin sauya tsarin a cikin gida.

By ukarofi