Sirrin masu zaɓe: ’Yan sanda sun tsare jami’in INEC da yi wa hadimin Wike tambayoyi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jami’an rundunar binciken sirri ta musamman ta ‘yan sandan Nijeriya (FID-IRT) da ke hedikwatar rundunar a Abuja sun fara gudanar da bincike kan yadda bayanan wani mai katin zaɓe na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) suka fito ba tare da izini ba.

Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, an tsare wani jami’in INEC da ke aiki a ofishin hukumar na Abuja Municipal Area Council (AMAC), yayin da aka gayyaci kuma aka yi wa Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Sada Zumunta ga Ministan Abuja, Lere Olayinka, tambayoyi dangane da lamarin.

Majiyoyin sun ce binciken ya samo asali ne bayan INEC ta shigar da ƙorafi kan fitar da bayanan sirrin wani mai rajistar zaɓe ba tare da izini ba.

A cewar majiyoyin, lamarin ya fara ne a ranar 29 ga Mayu, 2026 lokacin da wasu ‘yan siyasa suka gudanar da zanga-zanga a ofishin INEC na AMAC, suna zargin hukumar da rashin adalci a wani zaɓen fidda gwani.

Binciken ya nuna cewa bayan zanga-zangar, wani jami’in INEC ya gano cewa ɗaya daga cikin fitattun mutanen da suka jagoranci zanga-zangar, fitaccen jarumin Nollywood Emeka Ike, ya nemi sauya wurin rajistar katin zaɓensa daga Jihar Imo zuwa Babban Birnin Tarayya Abuja, amma har yanzu ba a amince da buƙatar ba a hukumance.

Rahotanni sun ce jami’in INEC ɗin ya fusata da zanga-zangar tare da wani bidiyo da Lere Olayinka ya wallafa a shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa ya aika masa da bayanan da suka shafi rajistar mai zaɓen.

An ce jami’in ya fara tuntuɓar Olayinka ta manhajar Facebook Messenger, daga baya kuma suka koma tattaunawa ta WhatsApp inda aka aika masa da takardar bayanan rajistar.

Majiyoyin bincike sun bayyana cewa bayanan da aka tattara daga wayoyin da abin ya shafa sun tabbatar da cewa an yi musayar saƙonni tsakanin bangarorin biyu.

A yayin tambayoyi, an ce Olayinka ya amince cewa ya wallafa bidiyon zanga-zangar a shafukansa na sada zumunta.

Ya kuma bayyana wa masu bincike cewa jami’in INEC ɗin ne ya tuntube shi, yana korafin cewa ana yi wa hukumar suka daga mutanen da ba cikakkun masu rajistar zaɓe ba ne a Abuja.

A cewarsa, jami’in ya yi alkawarin ba shi hujja ta hanyar aika masa da kwafin katin rajistar mai zaɓe, wanda daga bisani aka aika ta WhatsApp.

Masu bincike sun ce jami’in INEC da aka tsare ya amsa cewa shi ne ya fitar da bayanan, amma ya ce bai yi niyyar a wallafa su a bainar jama’a ba.

Shi kuwa Olayinka ya ce ba a sanar da shi cewa takardar da aka turo masa sirri ce ko kuma ba a yarda a yada ta ba.

Bayan kammala tambayoyi, ‘yan sanda sun bayar da belin Olayinka, amma sun bayyana cewa za a iya sake gayyatarsa yayin da bincike ke ci gaba.

A wani bayani da Hukumar INEC ta fitar, ta tabbatar da cewa binciken cikin gida ya gano asusun mai amfani da aka yi amfani da shi wajen samun bayanan.

Kwamishinan Hukumar kuma shugaban Kwamitin Wayar da Kai da Ilimantar da Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa an yi kutse ko satar bayanai daga tsarin kwamfutocin hukumar.

“Binciken farko ya nuna babu wata kutse daga waje a ma’ajiyar bayanan rajistar masu zaɓe, babu wani harin yanar gizo, kuma babu wanda ya samu shiga tsarinmu ba tare da izini ba,” inji shi.

Ya bayyana cewa an samu bayanan ne ta hanyar sahihin sunan mai amfani da kalmar sirri da aka bai wa wani jami’i da ke aiki a shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR), amma aka yi amfani da su ba bisa ka’ida ba.

INEC ta jaddada cewa lamarin ya shafi bayanan mutum guda kacal kuma bai shafi sama da masu zaɓe miliyan 90 da ke cikin kundin rajistar hukumar ba.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa Hukumar Tsaro ta DSS ta fara nata binciken kan lamarin, tare da alƙawarin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci bisa doka.

A halin yanzu, jami’an FID-IRT na ci gaba da kammala bincikensu, yayin da ake hasashen cewa za a iya gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu idan aka kammala tattara hujjoji

By ukarofi

Leave a Reply