Kakan Mohamed Salah ya rasu a Masar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Liverpool ta ƙasar Ingila, Mohamed Salah ya shiga jimami sakamakon rasuwar kakansa, Ahmed Abdel Aziz Al Bambi, wanda ya rasu a yau Litinin, kamar yadda rahotanni daga gidajen jaridun ƙasar suka bayyana.

Kawun ɗan wasan, Abdel Aziz Al Bambi wanda kuma shi ne shugaban cibiyar matasa ta Mohamed Salah, ya tabbatar da labarin rasuwar.

A wata taƙaitacciyar sanarwa, ya bayyana alhininsa bisa rashin, inda ya kuma nemi al’umma da su sanya shi acikin addu’o’insu wajen nema wa mamacin gafara.

Za a gudanar da jana’izar marigayin ne a babban masallacin Nagrig, wato mahaifar su Salah, inda ake sa ran samun halartar dandazon mutane.

Salah, wanda shi ne ɗan wasan Misra da ya fi zura ƙwallo a raga, ya buga wasan da Liverpool ta sha kaye da ci 2 da 1 a hannun Manchester City a ranar Lahadi.

By Babaji