Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jaddada sahihancin dakatarwar Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Litinin Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta tabbatar da matakin Majalisar Dattawa na dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ta ce majalisar ta yi aiki ne hukuncin doka akan al’amarin.

A hukuncin da alƙalai uku suka yanke a ƙarar da Natasha ta shigar akan Magatakardar Majalisar Dokoki Ƙasa da wasu mutum uku mai lamba CA/ABJ/CV/1107/2025, kotun ta ce dakatarwar ba ta tauye haƙƙin majalisa ko na kundin tsarin mulki da ya ba sanatar ba.

Abin da kotun yi shine soke tuhumar raina kotu da kuma tarar Naira miliyan 5 da aka ƙaƙaba mata, wanda ya shafi saƙon uzuri na barƙwanci da ta aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

A yayin karanta hukuncin jagora, Mai shari’a A. B. Muhammed ya ce Shugaban Majalisar Dattawa ya yi dai-dai da Dokokin Majalisar wajen hana Akpoti-Uduaghan magana a zaman majalisa na 20 ga Fabrairu, 2025, saboda ba ta zauna a kujerar da aka ware mata ba a hukumance.

Har ila yau, kotun ta jaddada cewa dokokin majalisar sun ba shugaban majalisar ikon sake rarraba kujeru ga ‘yan majalisa, kuma ana ba ‘yan majalisa damar yin magana ne kaɗai daga kujerun da aka ware musu, waɗanda kowane ɗaya daga cikinsu yana da ita.

By Babaji