
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani jami’in ɗan sanda mai muƙami kwanstabul, wato Mohammed Alhaji Muhammad, daga reshen rundunar na Jihar Borno, ya yi abin koyi inda ya mayar da kuɗi har Naira miliyan 2.6 da aka yi kuskuren tura masa ta asusun bankinsa.
A lokacin da yake miƙa kuɗin ga asalin mai shi, Alhaji Muhammad ya bayyana cewa ba zai taɓa cin moriyar abin da ba nasa ba, domin tarbiyya da tsoron Allah ne suka koya masa hakan tun yana ƙarami.
Ya ce, abin da ya ƙarfafa masa shi ne ƙoƙarin gyara mummunan fahimtar da wasu ke da ita game da ‘Yan Sandan Nijeriya tare da nuna cewa akwai jami’ai masu gaskiya da riƙon amana a hukumar.
Ya ce, “Na yi imani cewa idan kowa zai yi aikinsa da gaskiya, za a samu sauyi mai kyau a ƙasar nan.” Wannan mataki nasa ya ja hankalin jama’a da dama, inda da yawa ke yabawa jarumtaka da amincinsa, suna masu cewa irin wannan hali ne ya kamata ya zama ginshiƙin aikin gwamnati da tsaro a Nijeriya.”
Wannan al’amari darasi ne ga kowa musamman matasa cewa gaskiya da riƙon amana ba su taɓa sa mutum ya yi asara, saidai su ɗaga darajarsa a dukkan inda ya tsinci kansa.
