Arewa mai maƙiya da yawa

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Daga bara 2025 kamfen ɗin iƙirarin Hausa zalla ya ƙara bayyana don yadda masu ɗaukar nauyin makircin ke son a yi-ta-ta ƙare duk ko ina ma a ƙona ƙurmus. Siyasar 2023 da a ka yi shelar wai Musulmi da Musulmi ne su ka hau karaga na daga abun da ke ƙonawa ‘yan ƙaryar Hausa zalla rai duk da gaskiyar magana wallahi lamarin na cimma burin siyasa ne ba wai ƙarfin maida Nijeriya ƙasar Musulmi ba. Yo da Nijeriya ƙasar Musulmi ne akwai wani mugu da zai shiga daji ya riƙe makami ya na sace mutane a na biyansa kuɗi? Da musulunci a ke bi da akwai ɗan sullutun yaro da zai zagi Shehu Mujaddadi ya kwana a cikin wayarsa ta salula ya na minshari gwar-gwar..? Nijeriya fa na aiki da tsarin mulki ne na 1999 (gyararre) kuma tsarin bai hana Sheikh da Sheikh ko Reverend da Reverend tsayawa takara ba. ’Yan siyasa na ɗaukar salon da za su lashe zaɓe ne kuma su dau alkawarin kare tsarin mulki ba na Alkur’ani ko Bible ba. Adalcin tsarin ya ba wa kowa hurumin bin addinin da ya ke so ba tare da tsokanar mabiyin addinin da ba na sa ba.

Ta yaya wani zai fito ya ce lallai a yi MIDDLE BELT don wai yankin masu cin naman alade da kare ne wato ba Musulmi ba ne amma ya zo ya na sharhi kan Hausa zalla wai yaya za a tilastawa wata kabila ta yi hulɗa da wata? Ka ji neman tada sabuwar fitina. Biri ya yi kama da mutum waɗannan su ne kanwa uwar gami na farafagandar nan da abokan burminsu ‘yan zarmiya da ke son lallai a wargaza Arewacin Arewa don kafa kasar MIDDLE BELT da kuma biyawa wadanda su ke yi wa baranda ‘yan IPOB burinsu na kafa Biyafara. Wallahi akwai wani shaharerren ɗan farafaganda a Kaduna ta kudu da ke cewa in Biyafara ta balle za su yi ma ta mubaya’a.

A hankali wasu daga cikin ‘yan ƙaryar Hausa zalla na nuna kan su da kyamarsu ga addinin Hausawa wato musulunci. Masana sun yi gaskiya da su ka tabbatar da narkewar wasu ƙabilu masu bautar alloli zuwa Hausawa. Tabbas in ka kalli mutanen nan ka san ba rahamar Hausawa a jikinsu. Kai akwai ruhin Musulunci fa da kan bayyana jikin musulmi akwai na addinin Kirista da kan bayyana a jikin Kirista akwai kuma na bautar GIJI da kan bayyana a jikin matsafa. Sam-sam ‘yan iƙirarin Hausa zalla ba Hausawa ba ne amma su kan buya ba hoto ba sunan gaskiya yayin da za su watsa wannan guba ta murɗe wuyan tarihi da kuma babbar ajandarsu ta zagin Shehu Mujaddadi. Mutanen nan ba sa zagin kowa sai shugabannin Musulmi kuma sun dage sai sun yaki koyarwar musulunci ta nuna ƙabila ta fi addini daraja, ‘yan uwantakar ƙabila ta fi ta addini. Tun da sun fi mutunta ƙabilanci da addini su dau hanyar Reverend Shu’aibu Bargi ma na da su Farfesa Daniel Danladi Musa su ka ɗaurawa rawani na sarautar Hausawa Kirista na Kano. Kun ga ai a lokacin Daniel Musa bai ɓoye manufar ba, ya ce BAHAUSHE YA MULKI KANSA, shin mulkin kan nan shi ne Kiristoci su ware gefe guda Musulmi ma su ware?. Gaskiyar magana akwai kiyayyar bambancin addini a wannan farafaganda don haka mai yi da gaske ya fito fili ba buƙatar basaja sai dai in mutum dama rara-gefe ya ke yi matsoraci ne mai karyar gwagwarmaya.

Daga littafin FARAWA a tsohon alkawari GENESIS zuwa AYYUKAN MANZANNI a sabon Alkawari REVELATION babu inda wani kirista zai iya kafa hujja ta hurumin zagin shugabannin wani addini ko ma kai tsaye zagin Shehu Mujaddadi. In akwai ga kalubale a kawo ma na kuma na dau alƙawari duk wanda ya kawo hujjar hurumin ‘yan iƙirarin Hausa zalla su riƙa zagin Shehu Mujaddadi a cikin BIBLE zan amince da hujjar kuma zan daina magana a kai.

Daga taron naɗa Sarkin Hausawa mabiya addinin kirista na Kano ta fito fili kamar tsakar rana da ƙarfe 12 akwai hannun wasu mabiya addinin Kirista dumu-dumu a harkar Hausa zalla. Ina kira ga ƙungiyar Hauwasa Kirista HACDI ta ja wa Maguzawa da ke cikin tafiyar kunne su daina wuce gona da iri, gama ba su da hankali don in sun biyewa IPOB su ka kunnawa Arewa wuta har bukkokinsu ba za su tsira ba ko yadda IPOB su ka raina ‘yan Arewa ba za su karbe su a Biyafara ba. Waɗannan dai masu huluna, rawuna da doguwar riga su ne ‘yan uwansu har kiyama ta tsaya ko su na so ko ba sa so. Hakanan da wasu a ƙirƙirarren yankin MIDDLE BELT da ke cewa su na cin naman alade da kare wai su kenan ba Musulmi ba ne ba kuma ‘yan Arewa ba ne, su shafawa kansu ruwa don yankin na da miliyoyin waɗanda ba sa cin naman alade da kare.

Shugaban ƙungiyar Hausawa Kirista HACDI wato Farfesa Daniel Danladi Musa na jami’ar tarayya da ke Dutsinma jihar Katsina ya yi jawabi lokacin da ya ke jagorantar naɗawa Reverend Shu’aibu Bargi rawani inda ya nuna da hannunsu a kamfen din BAHAUSHE YA MULKI KANSA, ko yanzu a Arewa aljanu su ke mulki in ba Hausawa ba? Ga kalamansa a taron “’yan uwa, mu na kara yi wa Allah godiya domin wannan muradi na mu wanda mu ka daɗe mu na da shi. A matsayin Hausawa wanda waɗansu su ke tunanin ba za mu iya mulkar kanmu ba, to ga shi yau a jihar Kano mun samu asalin Bahaushe Kirista wanda ya zama Sarki na Hausawa Kiristoci na jihar Kano.”

Farfesa Musa duk wani abu da dan kasa zai nema ya yi hakan bisa tanadin tsarin mulki ta hanyar mutunta haƙƙoƙin sauran ‘yan kasa. Ina ƙara kira ga Farfesa a matsayinsa na Shehun malamin boko, ya yi amfani da kwarewarsa wajen tsabtace tafiyar ‘yan iƙirarin Hausa zalla Bahaushe ya mulki kansa. Kazalika duk waɗanda ke ɓoye ruff a wayar salula ba sunan gaskiya, ba hoto ba adireshi su bi koyarwar Yesu Almasihu su fito fili su daina makirci. Ba wanda zai iya kamawa ko hukunta duk mai gaskiya a ƙarƙashin dokokin Nijeriya. In ka ga mutum ya buya to makirci da mugun nufi ya ke da shi. Da fatan za mu ga canji.

Hatta wanda ya karanta hamshaƙin littafin MAGANA JARI CE na Dokta Abubakar Imam da kulawar Bature RM East zai san tsakanin Hausawa da Maguzawa hanyar jirgi daban ta mota daban. Maguzawa wasu ƙabilu ne a Arewa ‘yan gargajiya da su ka narke a jikin Hausawa kuma su na bin addinin Maguzanci da ke da babban alla mai suna GIJI mai kananan alloli gizagizai sai taimakon aljana Doguwa da sauransu. Ba wanda ya hana su bautawa GIJI kuma ba mai tsangwamar kowa kan addinin da ya zaba a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (Gyararre)

Har ila yau mai shafin nan na NIGERIAN BAHAUSHE wanda mun fahimci kowaye kuma za mu haska shi da tarihinsa da muradunsa; ya sake wallafa rubutu da ya ke cewa “Ina masu kiran Hausawa Maguzawa? Madalla da Maguzawa” Kun ga a nan marubucin na kokarin maƙala kansa ƙarfi da yaji ga Hausawa da ƙirƙiro tambaya wai ina masu kiran Hausawa Maguzawa. Ko a zantawar da na yi kwanan nan da masanin harshen Hausa Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya tabbatar da akwai wasu ƙabilu hatta a Kano da su ka narke su ka zama Hausawa. Tabbas biri ya yi kama da mutum don waɗannan ƙabilun da su ka taho daga wasu sassan Afurka na riƙe da addininsu na gargajiya kuma ba za su iya shiga musulunci ba don zai haramta mu su tsafe-tsafe, rawar banjo da bautar GIJI. Irin wadannan kabilun masu shigar burtu na kan gaba a sojojin da Turawan mulkin mallaka su ka dauka wajen yaƙi da Daular Sokoto su ka kashe ɗaruruwan mutane da fille kan su. Kaunar Bature ta sa wasu daga ciki sun karbi addinin Kirista amma har gobe akwai wadannan ƙabilu masu aron harshen Hausa su na shigar burtu da bautar GIJI kuma su ne su ka samu soshiyal midiya a bagas don ruruta fitinar ƙabilanci da zummar wargaza Arewa don cimma dogon burin taya abokan burminsu IPOB su kafa Biyafara da Midibelawa su ware wai su sam ba Arewa ba ne tun da ai Arewa an fiye sallah da salati su kuma ba sa so.

Mayaudarin marubuncin nan ya ce Maguzawa sun gina masallatai tun fiye da shekaru 700! Wanda ya gina masallaci amma ba ya sallah? Wallahi karya ya ke yi ya na kare tafarkin iyayensa ne kawai da cin zarafin addinin Musulunci. Wautar ita ce mutanen nan sun ɗauka in sun yaƙi Musulunci to sun yaƙi Shehu Mujaddadi ne. Ko ka ji dan IPOB na cewa THE BRAND OF ISLAM SMUGGLED INTO ZOO wai wani nau’in Musulunci da a ke amfani da shi a Arewa, ko in ya yi tatil da barasa ya ce ai Musulunci addinin Larabawa ne mu bar mu su kayansu mu koma gargajiya!. Wani ɗan Midibelawa don nesanta kan su da Musulunci ya ce alamarsu cin naman alade da kare.

KAMMALAWA

Mai ya sa Maguzawa ba za su fito fili su kafa wajajen bautar su ba su daina basaja? In Bamaguje zai gina masallatai to me ya sa ba zai gina wajen ibadarsa ta bautar GIJI ba? Ka ji soki-burutsu. Yo wadanda su ka gina masallatai fiye da shekaru 700 amma su na kamfen a soshiyal midiya na ƙabilanci da sunan Larabawa da hotunan karya ba adireshi? Akwai makirci. In ba fargaba ba su fito fili ma na, iyye ‘yan butan-uwa. Kai kai ku rufawa kan ku asiri don wallahi in na tono wani abu ko aikin nan na barandar IPOB da ku ke yi za ku yi murabus.

By ukarofi