A ƙasar mu Nijeriya, musamman yankin Arewa, zaman kashe wando da matasa ke yi na ci wa gwamnati da duk wani mai kishin cigaban matasa tuwo a ƙwarya. Mun wayi gari mafi yawan matasanmu basu da ayyukan yi. Yayin da wasu da dama sun gama karatun su na digiri a jami’o’i a fannoni daban-daban amma babu aikin yi.
Sai dai a maimakon waɗannan matasa su nemi ananan sana’o’i da za su yi, sai dai ka ga mafi yawan su sun raina ƙananan sana’o’i da ayyukansu, suna ganin in ba aikin gwamnati da za a biya su kuɗaɗe masu yawa ba, su zauna a cikin ofis mai na’urar AC da motar ofis; ba za su iya yin wani aiki ba.
Sun kashe zuciyarsu, sun ƙi yin wani aiki koma bayan haka. Harwayau, wasu sun fifita zama karnukan farauta na wasu ‘yan siyasa, wanda ake yi musu laƙabi da Turanci da ‘Data Boys’, wato waɗanda ‘yan siyasa ke saya musu data a wayoyin su na salula suna yaɗa muradun iyayen gidansu na siyasa da kuma cin zarafin duk wanda ya yi maganar ɓatanci a kansu. Data boys suna yawan yaɗa labaran ƙarya marasa inganci da baƙaƙen maganganu domin yaɗa ce-ce-ku-ce da ka iya jawo husuma, tashin tashina, da bata sunan wani ko kuwa ɓata wa wani siyasar sa. Bugu da ƙari, wasu matasan sun gwammaci suna sace-sacen kayan maƙwabta da na sauran al’umma, domin biya wa kansu buƙatunsu.
Wasu ma saboda lalacewa da mutuwar zuciya sun zama ‘yan a bi yarima a sha kiɗa wasu kuwa na maula a kasuwanni da masallatai suna faɗar ƙarairayi domin samun goyon bayan malaman addini, da fakewa a bayan addini ko ƙabilanci, don karkatar da hankalin jama’a zuwa ga masu gidansu. Wasu kuma sun zama ‘yan tumasanci da masu kai wa masu satar mutane bayanai kan maƙwaftansu. Wa’iyazubillahi! Wannan wacce irin mutuwar zuciya ce?
Muna zamani da aka samu cigaban fasahar sadarwa ta zamani, wacce ta zama tamkar walkiya mai haskaka ko’ina, akwai fasahohi kala-kala da mutum zai koya domin dogaro da kai. Wani lokuta za ka ga akwai masu son taimakawa waɗannan matasa ta hanyar horar da su akan wata sana’a ko kasuwanci ko taimaka musu da jari na kafa wata harka ta neman halal, amma abin takaici kasala da lalaci da ke damun wasu matasan ya hana su yaƙi da zuciyarsu.
Wasu kuwa in an basu jarin ko an horar da su akan wata fasaha ba sa yin abinda ya kamata da wannan gudummawar da aka basu ba. Wannan na daga cikin abinda ke ƙara kawo wa matasan mu koma baya.
Tashar talabijin ta TVC news ta gabatar da wani shiri na ‘Your View,’ inda ta nuna masu nazari kan al’amuran yau da kullum suna tattaunawa akan wani faifan bidiyo da Base TV ta wallafa a shafin ta na ɗ, wanda ya nuna wani matashi wanda ya koyi sana’ar hannun ta aikin shimfiɗa tayils amma rashin kayan aiki ta zama masa matsala. Sai ya kama aikin bola yana tattara wasu kayayyakin da aka yar masu amfani yana sayarwa. Bai dankwafar da kansa a irin mawuyacin yanayi na ƙasƙanci da wulaƙanci da wasu yaran talakawa ke samun kansu a ciki ba. Yana cikin wannan yanayin wani mai zuciyar tausayi ya share masa hawaye ya siya masa kayan aikin sana’a, ya saya masa waya salula kuma yayi masa kyautar dubu hamsin bayan ya saya masa tufafin sakawa.
Duk da yanayin da wannan matashi ya samu kansa, amma ya gina wa kansa rayuwa bisa ga tafarki mai kyau bisa ga tarbiyyar mai kyau da ya samu wajen iyayen sa. Bai ƙasa a gwiwa ba ya zama jajirtacce mai himma da kuma ƙoƙari. Ya yi wasu shekaru masu yawa yana kwasan bola domin tara kuɗin sayen kayan aikin tayils da kuma kuɗin da zai biya mai gidansa, domin samun ‘yancin kai ya je ya kafa kansa ta hanyar wanna sana’ar.
Abin lura a nan shi ne, muna da ire-iren waɗannan matasan masu ƙwazo da himma wajen sana’ar hannun. Amma babban abin da ya fi ci masu tuwo a ƙwarya shi ne basu da waɗanda za su ƙarfafa musu gwiwa ko kuwa basu agajin da ya dace domin cimma burinsu. Wannan na cikin manyan dalilan da suka sa muka fi tara ‘yan sara-suka, masu shaye-shaye, masu sace-sace da masu zaman kashe wando a Arewa.
A mafi yawan lokuta ’yan uwan mu na kudancin Nijeriya suke mana kallon cewa yankin Arewa ba shi da wani abin cigaba in banda tashe-tashen hankula da kashe-kashen mutane. Da fatan za mu yi koyi da irin waɗannan matasa masu zuciya, da masu halin taimako da imani irin wanda aka taimakawa matashin nan. Da fatan za a samu masu tausayi da halin da za su taimaka wa masu himma da ƙoƙari a cikin yaran talakawa da muke zamantakewa da su, domin cika musu burinsu.
A wannan zamani na cigaban fasahar zamani da muke ciki, akwai nau’ikan fasaha iri-iri wanda matasan Arewa suka koya, waɗanda kuma za su iya bunƙasa rayuwar su, kuma su samar wa kansu ci gaba. Zaman kashe wando da ƙwacen wayoyi da sauran harkokin ta’addanci za su ragu. Daga cikin abubuwan da matasan mu za su amfana da su a harkokin fasahar zamani, akwai ilimin zane-zanen na’ura mai ƙwaƙwalwa (Graphic design), ilimin tace hotunan bidiyo (Video Editing), tallace-tallacen zamani a shafukan sada zumunta (Digital marketing), ilimin amfani da shafukan sada zumunta domin inganta kowanne irin aiki ko kasuwanci (Social media management) da sauran su. Bugu da ƙari, yankin kudancin Nijeriya matasan su sun tsunduma wajen koyar waɗannan fasahohin zamani fiye da yankin mu na Arewa. Hakan ya samu ne domin masu magabatan su ba gwamnati da masu zaman kansu suna ƙarfafa musu gwiwa, samar musu da jari da ɗaukar nauyin ba su horo, don samar musu da sana’o’in dogaro da kai.
Haka zalika, yana da muhimmanci ga matasan Arewa su kasance masu himma da ƙoƙari wajen koyar sana’ar hannu da kasuwanci. A kullum mutum ya kasance yana tunanin yaya zai inganta kasuwancin sa ko sana’arsa ko kuwa amfani da ilimin sa ta hanyar da fasaha zamani za ta inganta masa harkokin rayuwarsa. Harwayau, masu ruwa da tsaki a Arewa suna da nasu kaso wajen ƙarfafa wa matasan Arewa gwiwa, domin ciyar da yankin gaba. ƙarfafawa ya ƙunshi samar wa matasa hanya ko kuwa tallafa musu da kuɗaɗe ko wata hanya da za ta ƙarfafa musu gwiwa wajen samar wa yankin Arewa cigaba mai ɗorewa. Haka zalika, masu ilimin sana’o’i daban-daban a unguwanni suna da nasu gudummawar da za su bayar wajen horar da duk matashi mai ƙwazo da himma akan sana’ar su. Wannan shi ne koya wa mutum yadda ake kama kifi ba yadda ake ci ba. Yin haka zai rage da yawa daga cikin ta’addancin da ke damun mu a Arewa.
Sannan a ƙarshe, gwamnati ta samar da ma’aikatu na horar da matasa akan sana’o’i da fasahar zamani ko ta zuba jari ta hanyar tallafa wa kowanne matashi da ke da hazaƙa da kuma himma da ƙoƙari, domin kawo wa yankin Arewa da kuma Nijeriya cigaba mai ɗorewa. Hassan Imran ya aiko da wannan wasiƙa ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected].
