Kamar Dogo Gide kamar Turji

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A cikin kwanakin nan kullum za ka ji labarin an sace takala ko mai kuɗi, kowa ma za a iya sacewa haka nan idan ƙaddara ta gitta za a yi iya rasa rai. Ko meye dalilin da ya sa lamarin satar mutane musamman a arewa maso yamma ya ƙi raguwa ko kawo ƙarshe?

Ni ma ban san amsar ba sai dai Allah ya kawo ma na sauƙi tun da duk matakan da hukumomi ke cewa sun ɗauka kama da ruwan wuta ta sama, tura sojoji dazuka da ma datse layukan sadarwar salula ba su sa an ji tsit ba varayi bailato. In na yi shiru sai nag a lalle wannan yaƙi na da wahala don ba kamar jan daga ta kare ƙasa daga wata ƙasa ko kutsen wasu ‘yan tawaye da ke zauna a wani waje ɗaya.

Gaskiya wasu ɓarayin a cikin ƙauyuka har ma birane su ke rayuwa. Ma’ana a nan su na samun garkuwa daga zaman su a wajen da fararen hula ‘yan ƙasa ke zama. Na ji akwai ma ‘yan ta’addan da kan halarci sallar Juma’a.

Don haka in dai buɗe wuta za a yi za a iya rutsawa da mutanen da ba su yi laifin komai ba. Wata matsalar ita ce ta jama’ar gari da kan ɗauki makamai don kare kan su amma wasun su kan iya amfani da damar wajen wuce gona da iri da kashe duk wanda ya yi kama ko da ta halitta ne da barayin daji.

Hakan ma ya sa a ke fatar mutane ba za su riƙa ɗaukar doka da hannu ba, don duk lokacin da ka ga fushin farar hula kan wanda ya yi mu su laifi yakan yi muni don bayan sun kashe sai sun datse kai.

Yanzu an ɗan sarara da jin sunan Dogo Gide wanda sunansa ya ƙara fitowa bayan labarin hallaka gagarumin ɓarawo Buharin Daji a jihar Zamfara. Yau labarin Bello Turji ake yi wanda har maulidin haihuwarsa ko irin wanda ake yi kamar yadda aka saba a shekara ya yi. Koma dai me za a ce addini ba shi da amfani a wajen masu satar mutane. Duk wanda zai sace ko ya kashe don samun kuɗi ko don wani ɓacin rai ai ya tube rigar Imani.

Hakanan illar barayin ta wuce neman kuɗi ta koma kisan gilla, fyaɗe da ma mafi muni qona mutane da ran su. Laifin me waɗanda a ke kashewa su ka yi wa ɓarayi. Wani ya tava cewa ai tun da shugabanni na zalunci kowa ma zai iya yin zalunci. Wasu kuma kan ce an raba su da dukiyar su ne don haka su ma sai sun rama.

To ramuwar a kan waɗanda su ka yi mu su zalunci ko kawai kan ƙaramar danga mai sauqin qetara. Ko ma irin faɗan nan da ke faruwa a jihar Filato ya kan zama baya ba zani don in kowa zai rama abin da a ka yi ma sa to faɗa ba zai tava ƙarewa ba kenan.

Kazalika, duk wata fitina a duniya in ka ga ta zo ƙarewa sai an zauna a kan teburin tattaunawa a samu maslaha. A lokacin da a ka kashe Buharin daji a jihar Zamfara an yi fatar hakan zai kawo maslaha ko rage fitinar amma ina sai ma lamarin ya ƙara ta’azzara.

Mugun yanayi a yankin Shinkafi da Zurmi ya isa abun misali cewa matsalar kamar ta kaucewa bakin zaren warwarewa. An ma ga gwamnatin jihar Zamfara na tattaunawa da ɓarayin don su ajiye makamai a yi sulhu su zama mutanen kirki. Hakan dai ba a san daga ina ya wargaje ba don gwamnatin ma ta dawo daga rakiyar sulhun ta wannan ɓangare.

Abin da ɗaure kai yadda a ke samun kwan-gaba-kwan-baya a wannan lamari. Kun ga fa fitinar ta faro ne daga satar shanu har ta koma ta gaggan ɓarayi ko ma a yanzu kamar yadda kotu ta yanke hukunci matsalar ta koma ta’addanci. A kowa ne yanki a ke samun wannan ƙalubale za ka ji an san madugun ɓarayin. Kuma alamu na nuna in an samu galabar ko shawo kan jagororin ɓarayin za a iya samun tsagaitawar wannan fitina.

Da alamun gajiya daga labarum hare-hare da kashe mutane, gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce, dubun babban ɓarawon dajin jihar Bello Turji na gab da cika. Wato ma’ana an kusa gamawa da shi ya zama tarihi. Turji dai na daga matasa masu ƙarancin shekarau cikin jagororin ɓarayin da a ke yi wa ta ke da KACALLA.

Gwamnan na magana ne a taron jama’a da ɓarayin ke gasawa aya a hannu, bayan ‘yan bindiga sun yi kisan gilla ga wani ɗan kasuwa a yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke kan gaba cikin yankunan jihar Sokoto da ke fama da ɓarayin ba ƙaƙƙautawa.

Hakanan ɗan majalisar dokokin jihar daga ƙaramar hukumar ta Sabon Birni Aminu Boza ya ce, lokacin da a ka datse layin sadarwa, ‘yan bindigar na amfani ne da layin sadarwar jamhuriyar Nijar, don haka matakin bai shafe su ba. Boza ya nuna sai gwamnati ta jajirce matuƙar dai za a ci galabar ‘yan bindigar da ke riƙe da manyan makamai.

‘Yan bindigar dai sun shiga ƙauyen Kurawa a Sabon Birni inda su ka yi kisan gilla a kan ɗan kasuwar mai suna Bello Yellow kazalika su ka sace mutum 5. An ba da labarin cewa ɗan kasuwar ya ƙi amincewa ya bi miyagun irin don a shiga daji da shi watakila a fara maganar miliyoyin kuɗin fansa. Bijire musu da ya yi ya sa su ka yi masa kisan gilla. Don an ce ma a harin ɗan kasuwar ne kaɗai ya rasa ransa.

Rahotanni a sahihan kafafen labaru na nuna babban abin takaicin cikin mutum 5 din 2 matan aure ne inda uku maza ne.

Gwamna Tambuwal ya yi taro da jama’ar yankin ne don bayyana mu su irin tsayin dakan gwamnati don gamawa da miyagun irin, inda ya ce, karyar Turji ta kusa ƙarewa. An zura ido kan gwamnatoci a ga sabbin matakan da za su iya ɗauka a sabuwar shekarar miladiyya ta 2022.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya nuna duk da ƙalubalen da qasar ke fuskanta na tsaro da cikas ɗin Korona, amma gwamnatin sa ta samu nasarori da dama.

Shugaba Buhari ya ce, abin da ya faru a baya ya wuce, amma alherin da ke gaba mai darajar gaske ne.

A rubutaccen saƙon shugaban na sabuwar shekara ta 2022 mai sakin layi 15, ya ce, a matsayin sa na mutum kazalika kuma shugaban ƙasa ya na damuwa ainun da yadda a ke samun taɓarɓarewar tsaro, ya na mai ta’aziyya ga ‘yan uwan jami’an tsaro da fararen hula da su ka rasa ran su sanadiyyar fitinar.

Muhammadu Buhari ya jinjinawa majalisar dokoki don amincewa da dokar sashen man fetur PIB a takaice da ta yi garambawul ga sashen; ya na mai cewa a bana gwamnatin sa za ta qara maida hankali kan kimiyyar yanar gizo wajen faɗaɗa hanyoyin tattalin arziki.

Ga shugaban matasa na tsohuwar jam’iyyar CPC da shugaba Buhari ya kafa Abubakar Maikudi ya ce, duk abun da shugaban ya aiwatar in dai ba ya bin sawu ba za a samu tasiri ba.

Shi kuma jigo a kamfen ɗin shugaban Aminu Madaucin Bakori ya aza alhakin wasu matakan da ke jawowa shugaban suka da rashin tasiri kan mukarrabai. Bakori ya ce, rashin tsarin da ya dace ne daga muƙarrabai ya jawo kushe shugaban don rashin zuwa Sokoto ta’aziyya maimakon haka ya tafi Lagos.

Shugaban dai zai share shekarar da bin kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 17.1, ya yi kwafa kan yadda ‘yan majalisa su ka cusa aiyuka 6,576.

Hakan na nuna kusan kowane ɗan majalisa zai tashi da kimanin aiyuka 14 kasancewar yawan dukkan ‘yan majalisar 469 ne.

A zantawa da a ka yi da shi ta wani shirin gidan rediyo, Ɗan Balki ya yi gargaɗin duk wanda ya makala kan sa kan shugaba Buhari zai taimake shi a kamfen ɗin 2023, ya sake dabara don guguwar Buhari ta lafa.

Kwamanda ya ce, ba gwamnatin da ta ba wa matasa jari da ta kai yadda shugaba Muhammadu Buhari ya yi, amma rashin tsaro ya sa tallafin ba ya tasirin da za a ga amfanin sa a ƙasa. Masu sharhi tamkar sun yi ittifakin inganta tsaro shi ne kawai mafita ga kawo cigaba mai ma’ana a Nijeriya da ke da ɗimbin arziki, amma ya kan maƙale a hanya ba ya isa hannun talakawa.