Kamaru: Shugaba Paul biya mai shekaru 93 ya naɗa ɗansa a mataimakin shugaba kuma shugaban sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya ya naɗa ɗansa Frank Emmanuel Biya a matsayin Mataimakin Shugaba kuma Shugaban Rundunar Sojin ƙasar, matakin da ya mayar da tsarin siyasa da jagorancin sojin ƙasar na bai-ɗaya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici da taƙaddamar zaɓe ke ƙara ta’azzara rikicin siyasa a faɗin ƙasar.

Nadin, wanda aka sanar a cikin wata doka a hukumance mai kwanan wata 4 ga Afrilu 2026, ya kuma ayyana Franck Biya a matsayin Wakili na Minista a Ma’aikatar Tsaro, wanda hakan ya sanya shi a tsakiyar tsarin tsaron Kamaru.

Matakin ya zo ne watanni bayan da aka rantsar da Biya, mai shekaru 92, a wa’adi na takwas da ba a taɓa ganin irinsa ba bayan zaben da aka yi takaddama a kai wanda ya haifar da zanga-zanga a faɗin kasar da kuma binciken ƙasashen duniya.

Paul Biya ya samu kashi 54 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaɓen, inda ya kayar da ɗansa takarar adawa, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya samu kashi 35 cikin 100.

Akan haka ne Tchiroma Bakary ya yi watsi da sakamakon zaɓen, yana mai dagewa akan cewa shi ne sahihin wanda ya lashe zaben bisa cancanta, sannan ya kuma zargi hukumomi da magudin zaɓe, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.

Biya, wanda ya mulki Kamaru tun shekarar 1982 bayan ya gaji tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Ahmadou Ahidjo, yanzu yana fuskantar sabon suka daga ‘yan adawa waɗanda ke zarginsa da ƙara ƙarfin ikonsa ta hanyoyin siyasa da na soja a ƙasar.

By Babaji