Fitaccen kamfanin tashoshin talabijin na MultiChoice ya miƙa wuya busa caccakar sa da ake yi, inda ya sake rage farashin biyan kuɗin DSTV da masu amfani da GOtV a Nijeriya, biyo bayan umarnin kotu da ta umurce shi da ya dakatar da yunƙurin ƙarin farashin.
Duk da cewa kamfanin na ƙasar Afirka ta Kudu ya dage kan ƙalubalantar hukuncin Kotun Kare Masu Sayayya da Gasa Tsakanin Kamfanoni ta Nijeriya a Abuja, MultiChoice ya rage farashi a manhajarsa a ranar Lahadi, 16 ga Yuni, 2024.
Bayan rafe farashin, yanzu masu amfani da DSTV za su biya Naira 29,500 maimakon Naira 37,000 na sashen Premium, yayin da masu amfani da sashen Compact+ za su iya biyan N19,800 a maimakon tsohon farashin N25,000.
Rage farashin zai sa masu biyan Compact Bouquet a kan N15,700, su biya fara biyan N12,500, yayin da masu amfani da Confam za su biya tsohon sabon farashin Naira 7,400 maimakon Naira 9,300 a kowane wata.
Ga masu biyan kuɗin Yanga, za a biya tsohon kuɗin N4,200 maimakon N5,100 da aka sanya a matsayin sabon farashi; yayin da masu amfani da Padi za su biya tsohon farashin N2,950 maimakon N3,600.
Haka abin yake ga masu amfani da GOtV waɗanda a yanzu ake buƙatar su biya tsohon farashin N12,500 na Super+ a maimakon N15,700.
Ana buƙatar masu amfani da GOtv Super su biya N7,600 daga N9,600, wanda kamfanin ya biya; Masu amfani da GOtv Max za su biya N5,700; GOtv Joli, N3,950; da N2,700 na GOtv Jinja.
